DDCDA ta Gargadi Masu Kunnen Kashi su Yi Taka Tsan Tsan ko Kuma su fuskanci Hukunci CDA ta Gargadi Masu Kunnen Kashi su Yi Taka Tsan Tsan ko Kuma su fuskanci Hukunci

Gwamnati bazata amince da Bata titi da kazanta ba da Kuma masu toshe Magudanun ruwa da shara da wadanda suke cin gefen kwaltaba domin Kara harabar gida ko shaguna ba

Matukar masu irin wannan Hali Basu dainaba Gwamnati zata Dauki Matakin hukunta dukkan masu kunnen Kashi hakan zaisa Gwamnati ,za,ta tauna tsakuwa domin Aya taji tsoro.

Wakilin gwamna Kuma maibawa gwamna shawara a Hukumar Raya birnin Dutse Alhaji Musa sule Dutse ya shaidawa taron manema labarai HaKa a wajan bikin kaddamar da kwashe shara na bana da Hukumar ta gudanar .

Musa Sule yaci gaba da cewar Gwamnati zata Dauki Matakin ladaftarwa akan wadanda suke sakin dabobi suna yawo akan titi suna haddasa hadari da Kuma masu shagunan sayar da maganin da suke sayarwa da matasa miyagun kwayoyi suna lalata masu Rayuwa .

Yakara dacewar Gwamnati zata aiwatar da komai bisa Doka da tsari Dan haka duk wadda ya taka doka za a dauki matakin hukuntashi komai girmansa .

Yaci gaba dacewar Gwamnati zata yi Anfani da Jami an tsaro wajan Garkame duk Wanda ya taka dokar da aka kafa wajan ganin an gyara birnin na Dutse domin tabbatar da sahihancin mahalli Mai nagarta a Jahar ta Jigawa.

Yakuma shawarci duk wadanda sukayi gine gone a gefen Titi Babu izinin Hukumar da wadanda sukayi gini akan magudanun ruwa su gaggauta cirewa tun kafin Hukumar ta waiwayesu

Yakuma gargadesu dasu kwashe yanasu yanasu tun kafin su fara Fuskantar bacinran Gwamnati bisa laifin da suka aikata, nayin gini ba bisa kaidaba ,yakara dacewar Gwamnati bazata sassautawa duk wadda ya taka doka ba

Tsohon Dan Majalissar Kuma maibawa gwamna shawara a Hukumar Raya birnin Dutse yakara da cewar Koda tsiya Koda tsiya tsiya Bazasu amince da duk Wanda ya taka dokar Gwamnati ba zasu hukuntashi komai matsayinsa

Shima dayake nasa Jawabin Shugaban Hukumar Raya birnin na Dutse Alh Madaki Abdulkadir ja ee ya bukaci hadinkan Al ummar Jahar Jigawa musamman mazauna birnin Dutse wajan tabbatar da tsaftar birnin na Dutse .

Yace yanzu HaKa suna da ma aikatan wucin gadi mutun 198 da suke aiki dasu Kuma zasuyi Anfani da kungiypyi masu zaman kansu domin ganin Shirin yakai ga Nasara

Ja ee ya shawarci Jama a su guji zuba shara barkatai amagudanun ruwa da gefen titi Gwamnati bazata lamunci wasu mutane suna aikata laifin ana kyalesu ba duk wadda Hukumar ta Kama Yana aikata laifin zai dandani kudarsa .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here