Gwamnatin Jihar Jigawa tare da hardin gwiwar kanfanin Mukaranta wanda ke samun tallafi daga kamfanin Bono Energy sun ware kananan hukumomi 12 domin aiwatar da shirin a makarantun 198 dake kananan hukumomin Jihar 12 daga cikin kananan hukumomin Jihar 27
Yanzu haka An kwashi malamai 240 wadanda da sune za afara wanna shirin na Mukaranta domin koyawa dalibai Rubutu da karatu amatsayin gwaji a daukacin kananan hukumomin Jihar 12 da za a fara aiwatar da shirin a Jihar Jigawa
Wannan Shirin za,a gudanar da shine a kananan hukumomin Ringim, Kazaure, Roni , Auyo ,Birnin Kudu ,Sule tankarkar, Garki, Hadejia, Gwaram, Birniwa,.Gumel da Babura.
Wakilinmu daya halacci wajan taron bitar da kanfanin Mukaranta da gwamnatin Jihar Jigawa ta shirya a cibiyar ilimi matakin farko ta Jihar Jigawa SUBEB domin wayar dakan malaman ya Sami ikon zantawa da wata Jami ar shirin Malama Hindy Muhammad daya daga cikin jagororin shirin harma tayi Masa Karin bayani
Tace shirin na Mukaranta mai taken literacy 4prosperity, Hausa liiteracy pilot programme for Jigawa state an fito da shinne domin ganin an ankoyar da dalibai karatu da harshen uwa
Takara da cewar manufar shirin shine koyawa dalibai karatu da rubutu a harshen Hausa saboda mahinmancin Hausa domin shine harshen uwa.
Takara da cewar wannan shirin zai kai tsawon wata 18 zuwa shekaru uku amatsayin gwaji a nan Jihar Jigawa wadda tuni aka baiwa malamai 240 horo Akan wannan shirin a daukacin Makarantun 198 da aka zaba afadin kananan hukumomi 12 da aka fara aiwatar da shirin anan Jihar ta Jigawa .