Bayan shafe watanni 23 a hannun Yan fashin daji Doge Gide ya saki Yara uku

Shugaban Yan fashin daji Daya addabi mazauna yankin zamfara yabaiwa yaransa umarnin su sako yarabuku daga cikin Yan Mata dalibai bakwai da suka rage na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke karatu a Birnin Yauri ta Jihar Kebbi da aka sace kimanin shekaru biyu da suka gabata Kamar yadda jaridar mu ta bankado .

Wadanda aka saki sun hada da Elizabeth Ogechi Nwafor, Esther Sunday da Aliya Abubakar.

Shugaban kungiyar iyayen ‘yan matan makarantar da aka sace, Malam Salim Kawoje, ya bayyana cewa sabbin ‘yan matan da aka sako sun isa birnin Kebbi ne da yammacin ranar Litinin, 8 ga wannan watan na Mayu, 2023.

“Eh sun sako mana uku daga cikin ‘yan matan makarantar ranar Lahadi da yamma. Tuni dai suna tare da gwamnatin jihar,” in ji Kawoje.

Sai dai bai bayyana ko an biya wani kudin fansa ba a lokacin dayake magana da Yan jaridu

Kamar yadda yake Karin haske yace ku tuna an sace Yara 96 daga cikin daliban FGC kebbi lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari makarantar a ranar 17 ga Watan Yuni, na 2021.

Yayin da wasu daga cikin wadanda aka sace suka samu ‘yanci jim kadan bayan kai harin, 11 daga cikin daliban sun kasance a hannun ‘yan bindigar.

Idan dai ba a manta ba, an sako hudu daga cikin ‘yan matan, da suka hada da Bilha Musa, Fa’iza Ahmed, Rahma Abdullahi da Hafsa Murtala daga hannun shugaban ‘yan fashin dajin, Dogo Gide a watan jiya.

Kawoje ya ce sun biya wasu makudan kudade da ba a bayyana adadinsu ba don ganin an sako ‘yan matan hudu bayan sun sayar da kadarorinsu da kuma wani asusu da ya sa ‘yan Najeriya da dama ke taimaka wa iyayen da kudi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here