Nigeria Bamai Hankali ,Bamai Barchi Saboda Talauchi da Rashin Tsaro-Aminu Ringim

Yan Nigeria kowa ya kone domin babu wanda Baya Shan wahala ,mutane Suna cikin masiba ta rayuwa data hada da Talauchi da Rashin tsaro .

Tsohon dan yakarar Gwamna a Jam,iyar NNPP Malam Aminu Ibrahim Ringim ya Fadi haka a shira da Manema labarai a gidansu dake Dutse a Wani taro da jam,iyar ta shirya da Nufin Fara yin adawa da gwamnatin apc.

Ringim yakara dacewar Gwamnatin apc batayiwa talakawa komai ba illah jefasu datayi a cikin kangin Talauchi da damuwa wadda kowa yake Fuskanta.

Aminu Ibrahim Ringim ya kara da cewar yanzu zasuci gabada Gudanar da taruka a daukacin kananan hukumomin Jihar 27 a ranar asabar mai zuwa kuma zasuci gabada yin taruka amazabu 287 da nufinyin adawa da gwamnatin apc mai mulki a Nigeria da Jihar Jigawa .

Yaci gabada cewar anfanin adawarsu shine fito da Gaskiya a fadawa gwamnati halinda jama ar kasa take ciki amatsayinsu na yan adawa bazasu ja baki suyi shiru ba alhalin gwamnatin apc tanayiwa talakawa gashin kuma ba.

Yaci gabada cewa jam iyar apc da gwamnatin su kowa ya gaza gane inda suka sa gaba domin gwamnati ce datake tafiyar kaguwa tana tafiya kamar kunkuru saboda Rashin alkibila cikin tafiyarta .

Malam Aminu yaci gaba da cewar yanada yakinin idan jam iyar NNPP ta amshi ragamar Mulkin Najeriya a 2027 zasu sauya akalar Nigeria domin zasu Fara cire talakawa daga kangin Talauchi wadda shine makasudin mawuyacin halin da yan Nigeria suke ciki .

Ringim ya kara da cewar matukar apc ce take Mulki a Najeriya kowa sai ya dandana kudarsa, yanzu saboda wahala yasa kowa ya fuskanci Gaskiya yan PDP da yan apc samada mutun 1000 suka sauya sheka muka amshesu ayau.

Alhaji Aminu Ibrahim ya kara da cewar yanzu a Nigeria bamai hankali ,bamai barchi ido biyu a rufe saboda Rashin tsaro Sakamakon bakin Talauchi da jama ar Nigeria suke ciki .

Yace matukar anason a zauna lafiya a Nigeria kowaye yake Mulki a Nigeria sauya kawar da Talauchi domin Talauchi shine ginshikin Duk wata matsala da jama a suke Fuskanta a halin yanzu .

Wannan yasa my yan adawa Mike kallon gwamnatin apc a Matsayin kabarin arne waje sumul, sumul ciki ba dadi .

Yakuma nuna damuwarsa Akan yadda Tsadar mai tasa Manoman Shinkafa mutuwar hasara a Jihar jigawa ,yakara dacewar Shinkafa ta girma tayi kyau Amma Rashin mai da Talauchi saboda Tsadar man yasa ala tilas Manoma sunbar shinkafarsu ta kone Bata nunaba

Saboda haka ya shawarci yan Najeriya su guji zaben tumun dare kamar yadda akayi abaya aka zabo gwamnatin apc mai Mulki ta jefa jama ar Najeriya cikin halin kaka nakayi

Yakara da cewar halin da yan Najeriya suke ciki san zuciyar mune yakaimu da kwadayi damuntsaya munyi zabe na Gaskiya munzabi mutanen da suka dace davamu Sami kanmu a halinda muke cikiba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here