Gwamnatin Jigawa zata Kashe Naira Miliyan N23.317m Domin horasda Malamai dabarun cin Jarabawa

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ware Naira miliyan Ashirin da uku da Dubu Dari uku da goma Sha bakwai N23,317 wadda akesa ran za a kashe wajan Horas da malaman Sakandire dabarun cin jarabawar WAEC da NECO ga daliban makarantun Sakandire

Gwamnati zata Kashe kudin ne wajan daukar Nauyin Masu bada horon da kuma malaman da za abaiwa horon Akan dabarun cin jarabawar ta NECO da Jarabawar WAEC wadda za a zana nan da wata biyu Masu zuwa

Jawabin hakan ya fitone daga bakin Dr Abbas A Abbas shugaban Hukumar Ilimin manya ta Jihar Jigawa wato Agency for Mass Education

Dr Abbas yayi wannan jawabin ne a wajan taron bitar da aka shiryawa Malaman Manyan Makarantun Sakandiren Gwamnati dake fadin Jihar ta Jigawa samada mutun 222 da aka zakulosu daga Makarantu Daban DAban aka shirya Masu bitar a dakin taro na sir Ahmadu bello dake cikin sabuwar sakatariyar Gwamnatin jahar jigawa kuma akesa ran kimanin dalibai 37,000 zasu anfana da bitar afadin Jihar ta Jigawa wadanda aka shirya bitar domin Anfaninsu wadanda akesa ran sune zasu zana Jarabawar karshe ta wannan zangon nan da wata biyu Masu zuwa.

Ya karada cewar Tsarin horas da Malaman an fito da shine tun lokacin gwamnatin data Gabata kuma zuwan wannan gwamnatin maichi ta Malam Umar Namadi ta dora daga inda waccan ta tsaya kasancewar tsari ne Mai kyau shiyasa ita wannan gwamnatin ta Rungumi shirin Hannu biyu saboda Mashinmancin sa .

Yakara da cewar wannan Yana Daya Daga cikin Manufar wannan Gwamnati Maichi wato 12 point agenda da gwamnatin Malam Umar Namadi ta tsara zatayi ,mu burinmu shine ace Jihar jigawa tana cikin sahun farko wajan cin jarabawar karshe a matakin Sakandire wato NECO da WAEC

Yaci gabada cewar su nasa ran kashi 75 na wadanda zasuci jarabawa ta NECO da WAEC a Nigeria dalibanJihar jigawa ne domin daga lokacin da aka fara horas da Malaman Jihar dabarun cin jarabawar zuwa yanzu Gwamnati tana ganin haske kuma anSami Gagarimin sauyi da cigaba wajan samun Yawan dalibai Masu Bazaka da suke cinyewa jarabawarsu a Jihar ta Jigawa sabanin shekarun Baya da da liban basa iya cin jarabawar.

Shima dayake nasa jawabin kwamashinan Ilimi mai zurfi na Jihar Jigawa Farfesa Isah Yusuf chamo yace Gwamnatin Jihar ta Jigawa ta shirya bitar ne da nufin horasda Malamai Dabarun cin harabawar ta NECO da WAEC a daukacin makarantun Sakandire dake Fadin Jihar ta Jigawa .

Ya karada cewar Gwamnatin Jihar ta fito da shirin ne domin ganin an Sami cigaba a harkokin karatu a fadin Jihar ta Jigawa .

Yakara da cewar Gwamnati ta ware makudan kudade Masu Yawan gaske domin daukar Nauyin shirin da Nufin horas da Malaman da zasu koyar da Daliban Makarantun Sakandiren dabarun cin Jarabawar wadda a kalla a nasa Ran kimanin dalibai 37,000 dubu Talatin da bakwaine zasu anfana .

Yabkarada cewar gwamnati dauki Malamai samada 1000 aiki domin koyarda Turanci da Lissafi wadda Yana daya daga cikin Manufofin wannan Gwamnatin na ta Inganta Harkokin ilimi a Daukacin Makarantun Jihar ta Jigawa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here