NDE Ta Horas da Matasa 50 Dabarun Kiwon da Noman Rani a Jigawa

Hukumar Samar da aikinyi ta kasa wato NDEReshen Jihar Jigawa ta zabo matasa maza da mata su 50 data basu horo Akan harkar noman Rani kiwon dabobi da kiwon kaji da Noman kifi da nufin inganta Rayuwar Matasan .

Matasan sun hada Maza 20 da Mata 30 da aka zakulosu daga sassa Jihar daban daban da nufin inganta Rayuwarsu

Shugaban Hukumar Samawa Mutane aikinyi ta NDE Alhaji Saadu Iya yarima ya Shaidawa Manema labarai haka Jim,kadan bayan baiwa Matasan horo a cibiyar Samarda aikinyin ta kasa Reshen Jihar Jigawa .

Alhaji yarima yace shirye shirye yayi nisa wajan Kaddamar da cibiyar baiwa Matasa horo mallakar Hukumar wadda akesa ran za a budeta domin fara baiwa Matasa horo.

Yarima yace gwamna Umar Namadi na jahar jigawa shine akesa ran zai kaddamar da sabon ofishin koyawa matasan Sana,pin Hannu a sati mai zuwa .

Ya karada cewar wadanda ake baiwa horon zasuyi tsawon sati biyu Suna samun horo kuma zasuyi sati 10 ana koyar dasu dabarun kiwon kaji domin su Zama kwararru Akan harkar kiwo da noma.

Domin haka ya hori matasan su tsaya stayin daka wajan koyan aikin ya kuma gargadesu dasu gujiyin fashi ko zuwa a makare yace Hukumar zata baiwa wadanda sukafi kwazo rancen Tallafin kudi da zasuyi Sana a domin su Zama Masu dogaro da kansu

Yakuma horesu dasu bada sabihan bayanai na asusun ajiyarsu su guji bada asusun ajiyar iyayensu ko samarinsu ko mazajensu da abokai Duk wanda baibada asusunsa ba bazasu Sami sakon kudin rancen da Hukumar tayi Masu alkawariba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here