Yan siyasa da Bankuna basa taimakawa harkokin wasanin a Jihar Jigawa

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ware Naira miliyan Dari biyu da hamsin N250 m domin gyaran filing wasa na Dutse shedikwatar jihar jigawa .

A yayin Gyaran Za a Samarda Karin gine gine irin na zamani da wurin Zama da fitilu da Sanya ciyawa itinta zamani a filin wasan domin yayi daidai da filin wasa na zamani da ake yayi a duniya

Shugaban kungiyar wasan kwallon kafa na Jihar Jigawa Alh Sabo Abdullahi Eka ya tabbatar da wannan labarin a lokacin da take ganawa da Manema labarai a filin wasa na Dutse  

Alhaji Sabo Eka  yaci gaba da cewar tuni gwamnatin Jihar ta ware makudan kudade da zatayi  Wani Gyara na wucin gadi a filin wasa na Dutse saboda Fara wasan kwallon kafa na kasa wato national lick wadda Nigerian lottery ta dauki Nauyin Gudanar da wasan afadin Nigeria .

Anasa ran za akashe kimanin Naira biliyan daya a daukacin wasanin da suke gudana a halin yanzu anan Jihar Jigawa wadda akesa ran kammalashi Ranar litinin mai zuwa, wasan da akayi kusan sati uku da farawa inji shi.

Alh Sabo eka yace gwamnati tana Gudanar da wassanine badan cin ribaba ko samun kudin shiga ba tanayine dominta rage zaman banzai a tsakanin Matasa kuma suma su Zama Masu dogaro da kansu da kuma Samawa matasan aikin yi wadda yin haka Yana taimakawa wajan rage yawaitar miyagun aiyuka a tsakanin al umma .

Yaci gaba da cewar yanzu gwamnati ta ware Naira miliyan hamsin domin gyaran filayan wasa na kazaure ,Birnin kudu Gimel,Hadejia da Ringim amatsayin Gyara na wucin gadi inda ko wanna filin wasan aka ware Mar naira miliyan goma kafin ayi Masu dukkan gyaran da suke bukata su Amsa sunansu na cikakkun filayan wasa kamar na kowacce nahiya.

Haka zalika gwamnatin Jihar zata kawata filayan wasa dake manyan Makarantu dake fadin Jihar kamar na Jami ar  FUD, jigawa poly ,yamidi da college education Gimel da sauransu .

Alh Sabo Eka ya kuma soki lamirin yan siyasa da Masu kudi dake cikin  Jihar ta Jigawa da cewar basa taimakawa harkokin wasanin a Jihar 

Alh Sabo yace Jihar Jigawa itace koma Baya wajan samun taimakon yan siyasa, yankasuwa da Masu kudi da bankuna wajan taimakawa a bunkasa harkokin wasa a Jihar .

Saboda haka ya bukaci gwamnatin Jihar Jigawa tasa baki wajan ganin bankuna da yan siyasa sun bada gudun mawar su wajan bunkasa harkokin wasa a fadin Jihar ta Jigawa .

Yace a Jihar jigawa ne kadai a Nigeria bankuna da yan siyasa basa Sanya hannunsu wajan bunkasa harkokin wasa a Jihar .

Ya nuna takaicinsa Akan yadda yan siyasa suke Sanya Matasa cikin harkar share shaye da jagaliyar siyasa mai makon Sanya matasan cikin harkokin wasa yadda zasu Zama mutane nan gaba a Rayuwarsu da za ayi alfahari dasu wajan bunkasa Tattalin Arzikin kasa kamar yadda wasu yan siyasa sukeyin  awasu jihohin na Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here