Karancin Ruwan sha yasa marasa lafiya da Masu zaman jiyya Garanba a asibitin Dutse

Karancin Ruwansha ya Addabi babban asibitin kwanciya na Dutse wato Dutse General Hospital ,lamarin dayasa marasa lafiya da Masu zaman jiyya gararanbar neman Ruwansha a unguwannin Maranjuwa, Fagoji Bakwato da bakin kasuwar yan Tifa dake Birnin Dutse

Kamar yadda bincike ya nuna takai takawo Marasa lafiya da Masu zaman jiyya sunkoma yin alwala da ruwan pure water na naira Ashirin kwaya daya da suke saya awajan Masu tallan ruwa saboda karancin ruwan Sha da asibitin yake Fuskanta .

Asibitin yafara fuskantar wannan Matsala ta Rashin Ruwa Kimanin tsawon mako biyu wadda Marasa Lafiya suke fuskanta, wannan matsala ta karancin ruwa a asibitin na general dake Dutse ya Zama babban al amari lamarin dayasa aka Sami kazanta a mafiya Yawan bandakunan dake harabar asibitin musamman wadda marasa lafiyar suke Anfani dasu hakan yasa marasa lafiya da Masu zaman jiyya yin fitsari da bahaya awasu sassa na cikin asibitin.

Wannan matsala ta karancin ruwa hatta fulawowin da aka dasa a wasu sassa na asibitin yasa sun shiga Mawuyacin hali yayinda fanfuna suka kafe karaf tamkar a sahara babu koda digon ruwa.

Da yake tabbatar da labarin shugaban asibitin Dr Abubakar Omonomo yace labarin Matsalar karancin Ruwan Shan Gaskiyane, yace Matsalar ta farune Sakamakon matsalar Rashin samun wutar lantarki kasancewar asibitin basa samun wutar lantarki kamar yadda ya kamata

Ya kara da cewar yanzu gwamnatin Jihar Jigawa ta Samar Masu da inji da zasuyi Anfani dashi wajan Samarda ruwan sha a asibitin yakumayi korafin cewar rijiyarsu ta Rufta tana bukatar yashewa wadda yanzu haka ana kokarin yasheta domin ganin Ruwansha a asibitin ya wadata

Ya karada cewar akwai bukatar gwamnati ta Samarda Karin Rijiyoyi a cikin asibitin domin ganin ansamarda wadataccen Ruwansha a asibitin da nufin kaucewa irin wannan Matsala nan gaba .

Yakuma Roki Marasa lafiya da Masu zaman jiyya dake kwance a asibitin dasuyi hakuri dangane da al amarin daya faru yace karancin ruwan ya farune saboda matsalar karancin wutar.

yace yanzu hukumomin asibitin da Hukumar bada Ruwansha ta asibitin sun dukufa wajan shawo kan matsalar wajan ganin an samar da Ruwansha a asibitin domin Anfaninsu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here