Kwamatin Mika mulki a Jihar Jigawa ya Mika Rahotansa

Yan kwamatin Mika mulki ga sabuwar gwamnati karkashin Jagoranci Lawan ya,u Roni sun Mika rahotan kwamatin ga Shugaban kwamatin Kuma gwamna Mai jiran gado Alh Umar Namaddi Dan modi

Hajia Rani Ishaq itace ta Mika kundin rahotan ga Zaɓaɓɓen gwamnan Jahar ta Jigawa Alh Umar Namaddi Dan modi a ofishinsa amadadin dukkan kwamatin

Dayake amsar rahotan kwamatin malam Umar Namaddi yace abinda yayi waccan gwamnatin shine yayi sabuwar gwamnati Babu batun wata matsala acikin tafiyarsu

Ya tabbatar da cewar Kamar yadda gwamna Badaru ya karasa aiyukan da tsobuwar gwamnatin sule lamido ta fara Bata kammalaba mu bamu da wata matsala duk abinda Badaru yafara Bai karasaba Zan kammalashi sannan na Dora daga inda ya tsaya inji gwamna Mai jiran gado

Domin Duk abinda wannan gwamnatin ta aiwatar tare dani akai Dan haka yazama tilas awajena na karasasu

Dan modi ya musanta batun cewar alkaluman sun nuna Jahar Jigawa itace tafi sauran jihohi talauchi yace tsohon labarine tuni alkaluman suka sauyi Kuma sunanan zasuyi iyakacin iyawarsa wajan raba Al,umma da talauchi ta hanyar samarda aiyukan da suka shafi Rayuwar Al,umma kaitsaye tareda inganta Rayuwar Al,umma ta fuskar Gina Dan Adam .

Yakuma musanta bayanin cewar ko akwai wata matsin lamba dayake fuskanta a siyasance yace shikan bashida irin wancan kalubalen da wasu zababbun gwamnoni suke fuskanta kasancewar su jam,iyarsuce take mulki Kuma sune suka sake samun Nasara Dan haka shibashida wata matsala

Daya Juya wajan rahoton Daya amsa yace kudin bayanan da aka bashi na kwamatin amsar mulki zai taimakamar wajan aiwatar da aiyukansa na gwamnati domin wata tirbace zaici gabada aiwatar da aiyukansa a aikace

Dayake Karin haske amadadin yankwamatin Alh Abubakar Sadiq Jallo wadda shine Dan Majalissar Mai wakiltar Karamar Hukumar Hadejia azauran Majalissar dokokin Jahar Jigawa yace gwamnatice dodar dazataci gabada aiki daga inda gwamna Badaru ya tsaya .

Yaci gabada cewar staying aiyukansu da kwamatin yayi na Yan kwanaki Basu Sami wata matsalaba Babu inda suka Sami wani bashi da akebin tsobuwar gwamnati Kuma Basu Sami wata matsalaba ko kalubale Yayin zaman kwamatin.

Yakara dacewar gwamna Badaru zai tafi yabar gwamnati Babu indayabar bashi ,atakaice ma zai barwa sabuwar gwamnati Yan kudade dazata farayin wasu aiyuka kafindai ace gwamnatin ta zauna da kafarta .

Sabanin yadda gwamnatin lamido ta barwa gwamna Badaru gwamnati Babu komai sai tarin aiyuka data fara Bata kammalasuba Amma duk da wancan kalubale munkarasasu kumaun aiwatar da namu aiyukan

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here