Bincike : Angano yayan makiyaya 23,000 basa zuwa makaranta a Jihar Jigawa

Kamar yadda bincike ya nuna Hukumar lura da ilimin yayan makiyaya ta Jihar Jigawa ta Gano kimanin Yara 23,000 ne basa zuwa makarantar afadin Jihar .

Shugabar Hukumar kula da ilimin yayan makiyaya ta Jihar ta Jigawa hajiya Ramatu Muhammed ce ta bayyana haka awajan kaddamar da makarantar yayan makiyayan akaramar Hukumar kiyawa aranar litinin data gabata .

Tace Kamar yadda bincike ya nuna yaran basa zuwa makarantar be sakamakon zuwa kiwo da yawan rikici dayake faruwa tsakanin Fulani da manoma da Kuma matsalar ambaliyar ruwa a lokacin damina

Hakan yasa ake samun sauye sauye wurin zaman makiyaya ma ana Laura daga wurin da suke zuwa wani sabon wuri domin nemawa dabobinsu abinci.

Hajiya Ramatu tace sakamakon haka yasa Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙirƙiro da makarantun tafi da gidanka guda biyar akananan hukumomin Guri,Gwaram ,kiyawa ,sule tankarkar da miga da nufin ilimantar da wadancan yara23,000 da basa zuwa makaranta.

Ta bukaci daukacin Al,umma su sani cewa yayan makiyaya ba kyamar karatun Boko sukeba sun Sami kansune acikin wannan Hali sakamakon Al,adarsu ta kiwo da Kuma da Kuma rashin makarantun akan hanyarsu ta zuwa kiwo.

Takara da cewar gwamnatin Jihar Jigawa ta dauki nauyin Bude irin wannan makarantun ne da nufin inganta Rayuwar yayan Fulani makiyaya dabasayin karatun Boko.

Hajiya Ramatu tace sun Gano wasu daga cikin iyayan Yara sunyi kaura daga Jihar Jigawa sun koma wasu jihohin dake makotaka da Jihar Jigawa ,wasu Kuma sun koma jamhuriyar Nijar saboda hakane gwamnati ta ƙirƙiro makarantun domin su Rika binsu duk inda suka Shiga su koyarda yayan makiyayan .

Yaci gabada cewar gwamnati ta dinkawa yaran kayan makaranta Mai alamar tutar Nigeria da nufin duk inda suka shiga Koda jamhuriyar Nijar ne za asan daga inda suka fito

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here