Jigawa da ,Zinder Sunsanya hannu akan kiyaye dokokin kasa da zaman Lafiya

Jihar Jigawa da Jihar Zindar ta jamburiyar Niger sun Sanya hannu akan yadda za a magance rikichin manoma da makiyaya Daya Jima Yana damun mazauna yankin chadi da Niger da jamburiyar Niger

Yarjejeniyar da jihohin biyu suka sanya hannu a Jiya Alhamis na kunshene da lura da hakkin makiyaya masu kiwi akan iyakokin kasashen biyu wato burtaloli

Dayake jawabi gwamnan Jahar Jigawa Alh Umar Namaddi Dan modi wadda mataimakinsa ya wakiltar awajan taron Alh Aminu Usman Rola yace yau tsawon Shekara hudu gwamnatocin biyu suna ta kokarinsa wajan kawo karshen matsalar makiyaya da manoma ayankunan biyu

Alh Namaddi ya Fadi hakane a wajan wata bita da kungiyar Ecowas ta shiryawa jihohin biyu wadda aka shirya adakin taro na M town hotel dake Dutse inda aka tattauna da masu ruwa da tsaki na bangarorin biyu wato manoma da makiyaya dakuma daukacin Jami an tsaro na dukkan jihohin Nigeria da Niger

Namaddi yace tsawon shekaru hudu gwamnatocin kasashen biyu sunata tattaunawa a tsakanin domin samarda sashihiyar mafita dazata magance yawaitar rikichin manoma da makiyaya Daya Jima Yana damun Jama a

Alh Aminu Usman yace wannan yarjejeniyar da gwamnatocin suka sanyawa hannu zata taimaka wajan samun dorarren zaman Lafiya tareda wayarwa dukkan bangarorin Kai tareda cigaban yankunan biyu dakeda makotaka da juna

“Daga yanzu akarkashin wannan doka da gwamnatocin biyu suka sawa hannu ,zamuyi aiki tare wajan kula da zirga zirgar makiyaya daga bangarorin biyu wajan kula da tafiye tafiyensu wajan tabbatar da tsaro a dukkan bangarorin biyu wajan tabbatar da cewar ansami raguwar hada Hadar Miyagun kwayoyi abamgarorin biyu .

“Kuma zamuyi aiki tare wajan inganta makiyayu tareda Kare burtalai wajan ganin ansamawa manoma da makiyaya hakkinsu yin hakane zai magance duk wata barazana da makiyaya me fuskanta musamman alokacin da makiyaya suke Kan hanyarsu ta dawowa ko tafiya wajan kiwo

Dan modi ya tabbatar da cewar gwamnati zatasa Ido wajan ganin dokar da suka sawa hannu tayi aiki kamar yadda akeda bukata

Dayake magana anasa jawabin gwamnan Jihar ta Zinder Malam Lawwali Amadou yace wannan yarjejeniyar tamkar wani ma aunine na gwaji wajan kula da zirga zirgar makiyaya wajan ketara iyakokin kasashen Africa

Yaci gabada cewar yarjejeniyar wato MOu tanada alaka da harkokin tsaro ,chigaban kasa da bunkasa tattalin arzikin kasa a tsakanin kasashen biyu saboda haka zamuyi iyakacin bakin kokarinmu wajan ganin dokar tayi aiki a tsakanin kasashen biyu

Anyi yarjejeniyar me tareda goyan bayan kungiyar Ecowas da Kuma dukkan kungiyoyin masu ruwa da tsaki dakeda alaka da kungiyar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here