Allah yayiwa Alh Bello Mai Tama Yusif Sardaunan Dutse Rasuwa ayau Juma a da sanyin safiyar Nan
Sardauna ya rasu Yana Daya daga cikin Manyan dattawa Arewa wadanda suka bada gudun mawa wajan ci gaban Nigeria kafin rasuwarsa tsohon sanata ne lokacin marigayi Sardauna sokoto shine Daya daka cikin mutane masu daraja da Sukayi minista har say uku a Nigeria Karo daban daban
An haifi Marigayi Bello Maitama Yusuf, a garin tsohuwar Gwaram, dake cikin jihar Jigawa 1947 ya rike mukamin Ministan cikin gida wato interior minister a 1981 da Kuma Ministan ciniki Minista a 1982.
Ya rasu yau Juma’a a jihar Kano yana da shekaru sittin da shida a duniya yabar Yaya Tara da jikoki masu yawa da matan aure
Wani Makusan cin Mamacin Alh
Alhaji Hussaini Dalhatu ya tabbatar da rasuwansa kuma yace zaayi masa Jana’iza bayan Sallar Juma’a a yau a masallacin Juma’a na fadar maimartaba sarkin Kano Sarkin Kano. Alh Aminu Ado bayaro anasa ran sarakunan Jihar Jigawa ,Kano Daura da Katsina sokoto da kaduna da Kuma yobe da Jihar Bauchi zasu halasci wajan janaizar
HaKa Suma gwamnatoci wadancan jihobi da Manyan Yan Boko da jiga jigan Yan Kasuwar zasu halasci wajan yimasa sallah afadar Mai Martaba sarkin Kano.