Gwamna Yahya Bello ya tsallake Rijiya da baya a hanyarsa ta zuwa Abuja

Gwamnan jihar Kogi, Abdullahi Yahaya Bello ya tsallake Rijiya da baya a wani yunkurin kashe shi da wasu ‘yan bindiga sanye da kayan sojoji suka yi a hanyar da ta zuwa Birnin Tarayya Abuja daga Lokoja zuwa Abuja.

Wakilinmu na Abuja ya rawaito lamarin ya zo a lokacin zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba cewar kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kingsley Femi Fanwo.

Ya ce an yi yunkurin kashe Gwamna Bello ne a tazarar kilomita kadan daga Abuja

An ce gwamnan yana kan hanyarsa ta zuwa wani aiki ne a Abuja daga Lokoka, babban birnin jihar Kogi, aka yi yunkurin kashe shi.

“Harin ya faru ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar Lahadi, 22 ga Oktoba, 2023.

“Maharan da ke sanye da kakin soji sun tare ayarin motocin Gwamnan suka yi ta harbe-harbe a kan motarsa da sauran motocin da ke cikin ayarin.

Sai da jami’an tsaro da ke tare da Gwamnan suka shiga cikin gaggawa domin dakile shirin sojojin da ba a san ko su waye ba.

“Hare-haren sun kasance a wurare uku daban-daban, shingen karshe ya kasance a kusa da babban birnin tarayya Kwali da misalin karfe 4:20 na yamma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here