Tsananin ,yunwa da Talauchi da jama a suke Fuskanta a Nigeria yasa Mutane da dama sun Mutu a layin rabon zakka a ofishin AYM Shafa da ke kan hanyar Jos ta Jihar Bauchi sakamakon kokawe kokawe Tsananin Mabuƙatan a Ranar lahdin data Gabata .
Ruhotanni da muka samu sun tabbatar cewa kimanin Mutane uku ne suka rasu, sai kuma wata majiya mai tushe da ta bayyana mana Waɗanda suka rasu sun kai mutane 17, waɗanda akasarin su mata ne da ƙananan yara kuma an kai gawarwakin waɗanda suka rasu Asibitin koyarwa na Jamiar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke Bauchi.
Cikin su akwai wata mata da yaronta da kuma wata matar da ƴaƴenta biyu, waɗanda rahotoni suka tabbatar duk sun fito ne don karɓar zakkar naira dubu biyar (N5,000) da ake bayar wa kuma tuni sun rigamu gidan gaskiya a sanadiyar gumurzun kokawar da akayi dasu awajan Rabon zakkar .
Bincike da wakilinmu ya gudanar, akan mutuwar Masu Amsar zakkar ya ce yawanci matane Masu karamin karfi inda da dama daga cikinsu a wurin suka kwana wasu kuma da asubahin fari suka halarci gurin don su kasance na farko a wajen karɓar zakkar.
An bayyana cewa jami’an tsaro sun yi iyaka ƙoƙarin su don hana turereniyar, amma yawan mutana ya fi ƙarfin su.
Wakilin namu ya tuntubi kakakin Rundunar Yan sanda ta Jihar Bauchi SP Mohammed Ahmed Wakil, ta wayar hannu don samun sahihin labarin da kuma tabbatar da adadin waɗanda suka mutu, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce a yanzu haka bashi da sahihan alƙaliman waɗanda suka rasu, sakamakon baya garin Bauchi .
” Sauka ta ke nan a filin jirgin saman Abuja ba na gari. Amma ina kan bincike daga DPO na GRA idan na samu cikakken bayani za asanar da Yan Jarida”. SP Muhammad ya faɗa.