Dan sanda abokin kowa sau da yawa idan an yi maganar dansanda abokin kowa kalmar tana da sarkakakiya ba kowane yake fashinta ba. Abinda ya sa ake cewa dan sanda abokin kowa shi abokin mai laifi ne kuma abokin mai gaskiya Ne. Domin mai gaskiya zai yi korafi a wajen dansanda kuma dansanda shi ne zai je ya kamo mai laifin. Za ka gan shi da mai gaskiya tare, kuma zaka gan shi da mai laifin a tare kaga duk wanda kaganshi tare dashi Abokin tafiyane .
Na fara ne da yi wa ‘yansanda kirari saboda irin aikinsu da kwazonsu a cikin al’umma sau da yawa nakan ji jama’a suna Magana akan ‘yansanda wani lokacin a fadi laifinsu wani lokaci kuma akan fadi jaruntarsu ko taimako da suka yi wajen kwato wa mai gaskiya hakkinsa a gaban sharia.
A wasu lokutan kuma sai ka ji wasu a gefe suna kalamai akan wasu bata-garin ‘yansanda duk dacewa ita duniya haka take babu yadda za a yi a ce kowa halinsa daya ne dana saura domin duk kyan aiki akwai Bata gari a cikinsu irin sune ake cewa wake daya Bata gari goma .
Yansanda sune zuciyar zaman lafiya a Nigeria domin a tarishin Najeriya sukadaine a jerin ma aikatan Gwamnatin tarayya bantabajin sunyi yunkurin tafiya yajin aiki a domin sune Najeriya in suka tafi yajin aiki babu sauran zaman lafiya ya kare sabo da haka yakamata a jinjinawa yansandan Najeriya ta fuskar komai.
Shikuwa kwamashinan yansanda Jihar Jigawa wato Ahmed Tijjani Abdullahi a fagen aikin dansanda gwarzo ne wadda samun irinsa zaiyi wahala bashida kwadayi kosan abin Duniya ba burinsu da yawa yanzu a Nigeria baizo aikin dansanda ba don ya Tara dukiya ba babban burinsu shine ya bunkasa aikin ya kawo cigaba a cikin aikin ,burinsa shine yasamar da Gyara a cikin aikin ya hana cuta facin hanci da Amsar Rashawa kuma ya tabbatar yabawa mai hakki hakkinsa ya tabbatar da Adalci a cikin aikin domin aikin dansanda shine kare doka da oda da baiwa mai Gaskiya gaskiyarsa shine babban burinsu.
Wannan yasa duk wurin daka zagaya a wuraren da yansanda sukeyin aiki tun daga shedikwatar yansanda zuwa kananan ofisoshin yansanda dake yankunan kananan hukumomi jahar jigawa duk inda kaga dansanda a cikin farin ciki yake ko dansanda mai kaki kokuwa na farin Kaya Yana cik wallwala bazaka gandhi a cikin damuwa ba saboda c p Abdullahi baichi amanarsu ba kuma ana kulada walwalarsà
Indai kaga dansanda Yana zage zage Yana korafi Akan AT Abdullahi wallahi baka bina bashin Rantsuwa Marar Gaskiya ne kokuwa lusarin dan sandane wadda bashida kishin kansas kuma bamai kishin kasa ba wadda baya kan tafarkin Gaskiya Amma Matukar Mutumin kirkine bazakiji komaiba abakinsa sai yabo da fadan Alkairi Akan shugaban yansanda na Jihar Jigawa
A gaskiya jihar Jigawa ta yi Kwamashinonin ‘yansanda daban-daban kuma kowanne akwai irin rawar da ya taka wajen cigaban jihar Jigawa Gaba a zamaninsa irinsu sale Ningi ,Bala Zama Sanchi irinsu CP Tilli da dai sauransu har zuwa wanda yake a kai yanzu wato CP Ahmed Tijjani Abdullahi.
Bahaushe ya ce kowa ya manta bara baji dadin banaba Amma Nikam a wajena a tarihi tunda aka yi Jihar Jigawa a 1991 babu Kwamashinan ‘yansanda da ya sanya aikin dansanda cikin tsari da tsafta da kare martabar aikin dansanda kamar wannan Kwamashinan na yanzu wato CP A.T. Abdullahi ya chanchanci a ciramar hula.
Kamar yadda bincike ya nuna shi kadai ne ya daidaita aikin dansanda a Jihar Jigawa cikin gajeren lokaci domin shi aikin ne a gabansa ba neman duniya ba. Yana zuwa farko ya gyada motocin fatirol domin ganin ya samar da tsaro a birnin Jihar
Haka zalika duk wata kafa ta munafurci ya tosheta kuma duk wadanda suka jima a wuri ya yi masu canjin wajen aiki. Hakkin ‘yansanda kowa ana biyansa hakkinsa babu maganar a kai ka aiki wani ya cinye maka alawus.
A takaice aikin CP A.T. Abdullahi aiki yake yi irin na ‘yansanda musulunci bai ci ba ba za su bari wani ya ci ba. Kowa ya tsaya akan aikinsa saboda haka yasa Gwamnatin Jihar Jigawa duk abinda ya bukata na tanadin aiki kamar man fetur motoci da duk wata gudunmawa ko ta kayan aiki ko abin hawa gwamnati ba ta kasa a guiwa wajen aiwatarwa dan ganin ansami Nasara.
Haka yasa ana samun tsaro sosai a Jihar Jigawa zai wahala Ka ji an ce an yi sata ko an yi fashi a Jihar tun daga lokacin da ya amshi Ragamar zama Kwamashinan ‘yansanda a Jihar Jigawa Allah Yana bada kariya da taimakonsa anayin Nasara .
Kowa ya sani yadda Hedikwatar ‘yansanda Jihar Jigawa take kafin zuwan CP A.T. Abdullahi ba ta da get mai awargaje yake tamkar ba shedikwatar tsaro ba kyau ba tsafta ba fenti babun ta yi yawa. Amma cikin kankanin lokaci ya tayar da gyaranta an yi wa kowanne ofis fanti an sake musu kofofi an samar fankoki da air condition a akowanne ofis an saka labulaye sabbi da sabin kujeru da tebura duk domin a samar da yanayin aiki mai kyau a wajen aikin ‘yansanda.
Zuwansa ya gyara masallaci ya gyara bandakuna nan da suka lalace an sanya garawul an yi land scaping a wurin sanya fulawowi. Domin kawata harabar Hedikwatar abin asha wa sai wanda ya gani kuma an samar da shataletale kanana a sassa daban-daban na cikin Hedikwatar. Yayin da duk wasu motocin ‘yansanda da suka jima a lalace aka gyarasu mai Anfani dasu wajan aiki.
A bangaren wadanda iyalansu suka rasu a bakin aiki ya yi iya kokarinsa wajen biyan Magada hakkokin mazajensu. Haka wadanda suka sami karin matsayi an kara musu. Wadanda hakkokinsu suka makale lokaci mai tsawo aka ki biyansu, ko kuma hakkinsu ya makale Basu Damina ya sa an biya su.
Yayin da wadansu yansanda suka makale a Fadar Gwamnatin Jihar Jigawa suka hana ruwa gudu suka zama tamkar kadangaren bakin tulu suma ya tarwatsa haka ya karawa aikinsa martaba a idanun jama ar Jihar Jigawa .
Yanzu in ka shiga Hedikwatar ‘yansanda ta Jihar Jigawa sai ka rantse da Allah kana babbar Hedikwatar ‘yansanda ta kasa ne dake Abuja Birnin tarayya saboda irin ayyukan da ake yi yanzu an sake wa Hedikwatar fasali tamkar shedikwatar tsaro ta yansandan duniya dake Birnin london
Nidai da nake Dutse dayake na kwana biyu ban shiga shedikwatar yansandan ba Saida naso nayi Batan kai saboda kyar na iya ganin ofishin kakakin Hukumar yansandan saboda kwalliya da akayiwa shedikwatar Saboda an gyara shi an sanya masa kayan kawa da Na,urorin kayan sadarwa irin na zamani da duk ‘yansanda suke bukata.
Canzawa shedikwatar fasali ba karamin aiki bane domin anyi kwamashinonin da suka zauna a Jihar Jigawa Amma babu mutun mai kishin Jihar Jigawa mai son Jihar Jigawa Kamar A T Abdullahi magana ta Gaskiya
Matakalar da zatakaika zuwa ofishinsa kuwa anyi mara ado da wani katako mai kyalli kuma anasa Wani tayil mai haske lamarin sai wanda yagani
Kafin ka kai ga fadarsa kuma wasu dakaru ne na Jami an tsaro Majiya karfi dauke da Ma yan makamai suke kaiwa Suna kawowa wato sintiri domin bada kariya. Yayin da a wajen amsar baki wato reception kuma wasu Matasa ne maza da mara suke Marhabin dakai a lokacin da ka sami nasarar shiga fadar domin Ganin kwamashinan yan sandan .
In ka je wajensa kuma kakarka ta yanke saka domin shi mutun ne mai fara’a da Jama a ga ikilasi kana zuwa zai tarbeka yabaka wurin Zama da Kayan Sha da makulashe Yana murmushi ku gaisa ya kuma sa a kawo maka ruwan sha musamman a lokacin da ba azumin ake yi ba.
Ni dai kam zan iya cewa Jihar Jigawa ta yi sa’a wajen samun Kwamashinan ‘yansanda wanda ya zo da shirin yin Gyara da tabbatar da aiki da son cigaban Jihar Jigawa don haka akwai bukatar jama a da sauran al umma sunayiwa kwamashinan yansanda da sauran Jami an tsaro hadinkai domin Ganin acigaba da samun zaman lafiya da tsaro mai inganci a jahar jigawa .