Wasu Mutane da ake zaton yan fashi ne sun Shiga Karamar Hukumar malam Madori sunkashe mutun biyu a wata unguwa da ake Kira sabuwar Abuja Kuma sun Rauna ta mahaifiyar su
Barayin dasuka aikata laifin da ake Zargin Yan fashine sunje gidan ita maman Yan biyu ne adaren jiya datsakiyar dare alokacin da sukaje gidan suka Bude wuta akan mutane gidan suka halaka yayan ta biyu
Barayin sun Kashe taro Mai suna Rechard Amos Dan Shekara 15 da kaninsa Cyril Amos Mai shekaru 12 a duniya Kuma sun harbii ma haifiyarsu a hannu ,inda sukaji Mata mummunan Rauni .
Yanzu haka dai Likitoci a Babban Asibitin Hadejia sun tabbatar da rasuwar su yaran yayinda ita Kuma mahaifiyar su take kwance tana amsar magani a Babban Asibitin Hadejia likitoci na yin iyakacin bakin kokarin domin ceton ranta
Kamar yadda Bincike yanuna ance mijin Matar wato maman Yan biyu dansanda ne wadda yanzu haka yanacan Adaya daga cikin jihohin da suke da matsalar tsaro a yankin sokoto a Nigeria Yana bada gudun mawarsa wajan Kare kasa
Hakan yasa wasu suke Zargin wadanda suka Kai harin gidanss ko wasune daga cikin Bata garin a wancan yankin daga cikin Yan ta addar da suyin fada dasu sukaje gidan nasa Shi Mr Amos sukayi ramuwar gayya akan iyalansa da nufin Cutar dashi .
Kakakin Rundunar yansanda na Jihar Jigawa Lawan shisu Adam ya tabbatar da faruwar Al amarin
Yakuma cigaba da cewar yanzu haka yansanda a Jahar Jigawa sun baza komarsu domin Gano ko suwaye suka aikata laifin domin kamasu a gurfanar dasu agaban Sharia