Wata jita jita Mai karfin gaske Tana kewayawa a Jihar Jigawa cewar gwamnan jihar malam Umar Namadi ya rufe asusun kananan hukumomi wai saboda akwai yiwuwar zai saukesu yanada kantomin riko aranar uku ga watan fabairu
Wannan jita jita ta tayarda hankalin shugaban,nin kananan hukumomi tareda dukkan magoya bayansu lamarin dayasa da dama daga cikinsu Suka shiga karatun ta nutsu wajan facaka da dukiyar talakawa
Takai ta kawo wasu kananan hukumomin basa iya gudanar da komai saboda tsoron mezaije ya dawo
Jin kunnenena naji shugaban wata karamar hukuma da banasan na anbaci sunansa anan yankin masaraitar Dutse yanayiwa wasu matasa jawabi cewar shifa bashida kudi suyimar hakuri Dan kudinsa na Sayan Maine a motarsa Kuma ko Sudinma suna mota basa jikinsa saboda gwamna ya rufe masu asusunsu Basu da ikon tabawa sai an bude masu asusun.
Yanayiwa matasan korafinne a lokacin da Suka tareshi a ofishin jam,iyar APC Jim kasan bayan da aka kaddamar da kwamatin yakin neman zaben injiniya magaji da,u Aliyu a ofishin jam,iyar
Saboda hakane ma wakilinmu ya tuntubi shugaban jamiyar ta APC domin jingaskiyar labarin cewar wai gwamna zai sauke ciyamomin kananan hukumomin jihar 27 Kuma zai nada kantomomin Riko shiyasa ya bada Umarnin a rufe asusun kananan hukumomin jihar 27
Alh Aminu Sani Gumel wadda shine shugaban jam,iyar ta APC a Jihar Jigawa yakada baki yace wannan labarin bashida tushe balantana makama labarine na Kazan kurege ba ayishiba Kuma Babu alamunsa
Yace shidai abinda ya Sani za ayi zabe awatan shida Mai zuwa Nan gaba kasan Kuma haryanzu gwamna baibada Umarnin ciyamomin kananan hukumomi suyi fastaba ko tallan kansu yakara dacewar batun kantomomi Kuma Babu wanan maganar shidai amatsayinsa na shugaban jam,iya baisantaba