Bayan daukewar Ganina tsawon Shekara Biyu Ganina ya dawo – Hassan Didan Dango

Wani tsoho Mai Kimanin shekaru 90 da haihuwa a duniya mazau nin kauyan gidan dango a gundumar Aikata dake cikin yankin Karamar Hukumar Jahun Mai suna Hassan wadda ya makance tsawon shekaru biyu baya gani Ganinsa ya dawo bayanda akayimar Aikin gyaran Ido a Babban Asibitin gwamnatin Jahar Jigawa dake Dutse

Dayake Zantawa da manema labarai Bayan yimasa Aikin gyaran idon malam Hassan yace yunwa ce a wani lokacin take makan ta Mafiya yawan Jama a ba a saniba ba makantace ta hakikaba .

Malam Hassan yace tsawon shekaru biyu da yayi Yana Famada Cutar makanta a kauyansu ko wanka zaiyi baya iya Kai kansa bandaki sai matarsa takaishi saboda baya iya gani HaKa zalika idan zaiyi ba haya baya iya zuwa bandaki saita matarsa ta kaishi ta dorashi adaidai wurin dazai yi ba hayar.

Malam Hassan gidan dango yakara dacewar rashin abinci Mai kyau da Kuma ƙarancin abinci na Rayuwar yauda kullum Yana taimakawa wajan makance war Al umma a yankunan karka ra

Hassan yace Mafiya yawan mutane da suke Famada larurar rashin gani mutanen kauyene da suke da matsalar ƙarancin abinci Mai Gina jiki sai Kuma matsalar shekaru insunyi yawa tsofi masu yawan shekaru Suma sunada matsalar

Malam Hassan yakara da cewar kafin ya Sami larurar rashin gani ya taba Zama malamin makaranta a kauyansu badan iyayen sune suka ciresu daga makarantar boko ba da Yana Daya daga cikin manyan Malaman makaran tar Boko a Jihar Jigawa da Gwamnati Zatai alfahari dasu

Yaka ra dacewar Yana Daya daga cikin wadanda suka Bude makaran tar Boko ta Farko a Karamar Hukumar Jahun tun zama nin tsohuwar Jahar Kano a zama nin sarkin Kano Sunisi na Farko

Yace lokacin Daya kamu da larurar ciwon idonsa ya farane da matsalar kai kayin Ido hartakai idon sa Yana ruwa wata rana HaKa kawai ya wayi gari baya gani idon sa ya rufe baya gani

Malam Hassan ya kara dacewar alokacin da likitocin suka yimar aiki ganinsa ya dawo saiyaji tamkar Yana Wata Sabuwar duniya ne saboda farin cikin da zumudi

Ganin yadda likitan dayayi Mar aiki ya Sami Nasara akaisa wajan dawowar Ganisa yasa likitan Bai sallame shiba yace Daya idonma saiya dubashi yanzu dai anyimasa aiki Ganinasa ya dawo bashida Wata matsala

Yakarada cewar Babu abinda zaice da gwamnatin Jihar Jigawa da hukumar data dauki Nauyin yimasu Aikin gyaran idon sai fatan da fatan Allah ya biyasu duniya da lashira

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here