Danmodi Zai Inganta Tsarin Nomas A Jihar Jigawa Zuwa Tsarin Noman Zamani – Maigatari

Zuwan Gwamnatin Malam Umar Namadi cikin wata biyar an sami sauyi a cikin tsarin harkokin noma a Jihar Jigawa. Domin Manoma sun jima suna shan wahala akan tsarin noma domin su iya cigar da kansu, amma ba sa iya cigar da kansu.

Da zuwan wannan gwamnatin ,gwamnatin Malam Umar Namadi ta bullo da tsare-tsare masu ma’ana da za su taimaka wajen sauya alkibilar noma ya zama noma na sana’a a Jihar Jigawa.

Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Kasuwancin Aikin Gona JASCO Alhaji Rabi’u Khalid Maigatari ya tabbatar da haka a wata ganawa da ya yi da manema labarai a ofishinsa.

Ya ce yanzu shirin da gwamnatin Jihar Jigawa ta bullo da shi na inganta tsarin noma ya wuce inda manoman suke tunani ana son manoma su mayar da noma sana’a ne su daina tunanin yin noma domin abincin da za su ci kawai.

Ya cigaba da cewa gwamnati za ta bullo da tsare-tsare za ta samar da iri mai nagarta wanda yake da saurin haihuwa domin amfanin manoma wadda hakan zai taimaka wajrn samun Amfani mai yawa.

Ya ce mutane shaida ne dalilin zuwan gwamnatin Malam Umar gwamnatinsa ta rage farashin taki, a lokacin buhun taki naira 26000 ta sauke farashin ya komo naira 16000 domin a saukaka wa manoma saida aka sauke tirela 200 da yawa manoma sun saya sun a jiye Saboda noman rani. saboda suna tsoron ko ba za su sake samun irinsa ba.

Ganin haka ya sa gwamnati ta sake tanadin takin domin sake sayar wa manoman rani a kan farashin mai sauki domin ganin an yi noman rani cikin sauki.

Yanzu haka gwamnati ta sa yi maganin feshi da injinan feshi da taraktocin noma manya. Sannan kuma ta shigo da kananan motocin noma na hannu wadanda kananan manoma za su yi Amfani da su a gonakinsu domin saukaka wa kananan manoma kuma a inganta harkokin noman a Jihar Jigawa.

Maigatari ya ce yanzu manoma a Jihar Jigawa sunayin noma ne cikin kwarewa kasancewar yanzu duk fadin Nijeriya babu wata Jihar da takai Jihar Jigawa fadin kasa mai albarkar ruwa da dausayi da manoma za su yi Amfani da kasarsu wajen yin noman shinkafa da na alkam. Ya karabda cewa yanzu Jihar Jigawa tana iya noma shakta 70,000 ta alkama a Shekara. Kuma idan aka bai wa Jihar dama za ta iya ciyar da Nijeriya ta fannin noman alkama da shinkafa. Domin Jihar Jigawa tana da dajin da za ta iya noma alkama da shinkafa sama da shakta 200,000 a shekara.

Kamar yadda bayanai suka nuna inji shi ya ce manoman Jihar Jigawa sun sami shaida a wajen Gwamnatin Tarayya ba sa jin biyan bashi. Sannan kuma suna amfani da shawarar malaman gona yayin aikin gona shi yasa ba sa samun matsala a lokacin da suke yi noma.

Ya ce Danmodi abin a gode masa ne domin ya kawo sauyi a cikin tsarin noman zamani a Jihar Jigawa ya raba manyan taraktocin noma wadanda rabon a ga irinsu suna aiki a gonakin talakawa a Jihar Jigawa ya fi shekaru 20 da suka wuce. Amma yanzu an kawo su sunayi wa manoma aiki ba dare ba rana a Jihar Jigawa.

Shirye-shirye sun yi nisa gwamnati za ta shigo da injinan gyaran shinkafa wadanda za ta rabawa manyan manoma a kan farashin mai sauki su kuma za su yi Amfani da su wajen yi wa kananan manoma aiki a gonakinsu. Hakan zai taimaka wa manoma wajen samun riba a noman alkama an daina casar alkama da shinkafa. Wannan inji shi ne zai cashe alkama da shinkafa sai dai a zuba a buhu don haka manoma za su yi dariya.

Da ya juya wajen irin agajin da gwamnati za ta bai wa manoman saboda tsadar man fetur ya ce gwamnatin Malam Umar Namadi ta shigo da injina masu aiki da hasken rana za ta raba wa manoma bashi akan farashin Mai rahusa za su yi Amfani da su wajen noman alkama da na shinkafa ‘yar rani. Kuma za ta tona wa manoman rijiyoyin a gonakinsu kyauta domin gudun kaucewa hasara tare da bai wa manoma taki da irin alkama bashi akan farashi mai sauki.

Kuma gwamnati ta kafa kwamatin wanda shi ne zai raba kayan. Kuma shi ne zai amso bashin da aka bai wa manoman domin gudun kada a sami wata matsala daga wajen manoman da aka baiwa kayan noma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here