Fried haulers tayi shirin.samawa matasa 540 aiki a Jihar Jigawa

Da yake Jawabi ga Manema labarai Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Tara kudaden haraji da harkokin sufuri ta kasa Reshen Jihar Jigawa frieds haulers Association of Nigeria Alhaji Bala Abas yan,kwashi

Yace ita kungiyar fried haulers Babu dabo ko bakin ciki a cikin ta Kuma Babu yaudarar ko karya a tsarin ta gaskiya zata fito fili a lokacin da iyayan kungiyar Nan sukazo kaddamar damu anan Dutse duk wadanda Basu Shugoba zasuso sushiga a lokacin daba zasu iya Shugaba domin sunyi wasa da damar su

Zamu gudanar da Gagarimin taro a Nan Babban birnin jaha a lokacin da za,a kaddamar damu zamu dauki Ma aikata ashirin 20 a kowacce Karamar Hukumar daga cikin kananan hukumomi jihar 27 da muke dasu

“Inka hada gaba Daya zamu dauki matasa 540 Kuma munada mutane 16 a kowacce Karamar Hukumar ma aikata wadda yawansu yakai mutun 354 kaga akallah min Samarda aikinyi ga mutane kusan dubu saboda haka fried haulers zata kawo cigabane a Jihar Jigawa ta fuskar inganta tattalin arziki da Samawa Jama a aikinyi” .

Dan haka ya nemi hadin Kan Jama ar da suke cikin kungiyar su bashi hadinkai Dan ganin kungiyar takai ga Nasara ,yaci gabada cewar duk Nigeria Babu kungiyar datake da tsari Kamar fried haulers domin it’a kungiyace da Babu bakin ciki a cikinta ko cutarwa tana gudanar da komaine a Bude kamar yadda ma aikatan banki sukeyi komai a.cikin tsari

Yaci gabada cewar kungiyarsu inta fara aiki hatta masu talla akwai irin harajin da zasu amsa a wajan haka Kuma zasu karbi harajine awajan wadanda suka chanchanci su biya harajin kasa daga kan matukin Keke zuwa Kan matukin jirgin sama da jirgin kasa Dana Ruwa kowa sai ya biya .

Hakan zalika masu kananan kanfanoni da Manya aduk Inda suke afadin Najeriya yazama Dole su biya harajin a ma tsayin dukiyar kasa.

Yakuma shawarci yayan kungiyar a matakin jiha Dana kananan hukumomi su marawa kungiyar baya Dan ganin takai ga Nasara ,haka.zalika ya boresu Dasuyi iyakacin kokari su kammala biyan kudin rijistar yayansu amatakin kananan hukumomi yace domin idan sukayi sakaci kungiyar zata iya kubucewa daga wajansu

Dayake jawabi shima ma ajin kungiyar na Jihar Alh Usman Abdullahi ya hori yayan kungiyar suyi kokarin kammala yin rijistarsu cikin lokacin da aka.ware duk Karamar Hukumar datayi sakaci Batayi rijista da wuriba suka Bari wasu suka Shiga sukayi rijista damu ayankinkinsu zasu koma Yan kallo

Yace makasudin taronshine awayrwa yayan kungiyar Kai Kuma afadakar dasu Mashinmanci yin rijistar zata taimaka wajan Samawa matasa aikinyi zamu daukewa ita Kanta gwamnatin Jahar Jigawa wani nauyi Daya kamata ace itace yakeyi wajan baiwa matasa aikinyi

Da yake nasa Jawabin sakataren kungiyar a Jihar Jigawa Malam Isyaku Umar Dan,zomo ya hori yayan kungiyar a duk inda suke su hada kansu kada suyiwa juna kyashi su Zama masu amincin da kaunar juna wajan yin aiki tareda Nemawa cibiyar cigaba .

Malam Isyaku yakara da cewar haulers Nan bada dadewa ba zata kafa ofishinta anan Jihar Jigawa Kuma zata dauki matasa sama da mutun dubu Daya Aiki domin fara amsar Haraji

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here