Gwamnati Ta Sayi Kayan Abinci Tirela 110 Saboda Korar Yunwa A JigawaDaga Umar Akilu Majeri Dutse

Gwamnatin Jihar Jigawa ta sayi shinkafa tirela 70 da masara tirela 40 domin taimaka wa talakawa da suke fuskantar matsin rayuwa a Jihar sakamakon cire tallafin Mai da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Gwamna Umar Namadi ya shirya haka ne domin korar yunwa daga fadin Jihar ta Jigawa baki daya.

Shugaban Hukumar Samar da Agajin g
Gaggawa na Jihar Jigawa Alhaji Haruna Mai Riga ya tabbatar da haka a wata ganawa da ya yi da manema labarai yau a ofishinsa da ke Sakatariyar Jihar.

Mai Riga ya cigaba da cewa gwamnatin Jihar ta gina ganuwar dole domin hana ruwa ambaliya a daukacin wuraren da ruwan yake wa jama:a barazana a duk shekara.

Kuma an shirya wa mazauna kauyuka dabarun kare kansu. Kuma gwamnati ta tanadi makarantun gwamnati a matsayin sansanin wadda ruwa ya raba da mahalinsu. Kuma an gina bandakuna da magunguna da nufin kare lafiyar wadanda za a ajiye a wurin.

Hakazalika Gwamnati ta yi tanadin abinci domin ganin Gwamnati ta kori yunwa a fadin Jihar gaba daya.

Kwamatin SEMA ya ziyarci wuraren da aka yi aikin badalar dole wadda aka tanada da nufin kare garuruwa daga barazanar ambaliya a Kananan Hukumomin Jahun, Taura, Miga da Ringim.

Ya kara da cewa Gwamnatin Jihar Jigawa ta hada guiwa da Geamnatin Tarayya da kuma Kananan Hukumomin Jihar 27 wajen sayan kayan da za a raba wa al’ummar Jihar.

Ya ce wannan karon Gwamnati za ta raba kayan abincin ne ga daukacin al’ummar Jihar babu maganar a bai wa wasu a hana wasu. Amma za a bada fifiko ne ga Marayu da Nakasassu da Marasa karfi wajen rabon kayan abincin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here