An yabawa Gwamnan Jihar Jigawa Alh Umar Namadi FCA Bisa na Mijin kokarinsa wajan in ganta Harkokin karatu a Makarantar kiwon Lafiya ta Jahun wato College of Health Technology Jahun.
Kamar yadda Tarishi ya Nuna Babu wata Makarantar kiwon lafiya da take koma baya a fadin Najeriya Kamar ta Jahun bincike ya Nuna a fili itace Makaranta Mafi Tsufa tunda akayi jihar Jigawa Amma Kuma ita kwalejin da Bata Sami cigaba ba.
Hakan yasa mahanlta suka sake yabawa gwamna Namadi bisa Irin kokarinsa na Ganin an Inganta Makarantar Data Jima a cikin kunci Tsawon shekaru Masu yawa babu cigaba Mai yawa tamkar ba Jami a ba.
kasancewar duk wasu Jami,oi da akayi abayanta sunyi Mata fimtinkau ta fuskar cigaba irin na zamani .
yanzu kam zuwan wannan gwamnatin ta malam Umar an samqrda Rassa har guda biyar acikin Makarantar da suka Hada da school of health science da school of health information Management da school of Enviromental health science da school of community health da Kuma school of General study
Wakilinmu yayi bakin iyaka kokarinsa wajan samun shugaban makarantar Malam Abdullahi Abubakar Mai Rikon Gado akan irin Yadda gwamna Namadi take kokarin wajan sanarda cigaba da sauyawa makarantar fasali Mai ma Ana domin ganin ansaka komai a mahallin daya dace .
Shugaban kwalejin na Riko wato Malam Abdullahi A ubakar ya yabawa gwamnatin jahar Jigawa akarkashin Jagorancin Malam Umar Namadi akan Irin kokarin da gwamnatin ta keyi wajan Samarda aiyukan cigaba a Makarantar Kamar yadda aka Ciyar da Sauran Jami o in jahar Gaba Suka amsa sunan su na Jami oi da kwalejin .
Malam Abdullahi Abubakar Yaci Gabada cewar yanzu haka shirye shirye yayi Nisa wajan Samqrda Sabbin Dakunan kwanan dalibai Na Maza Benaye irin na zamani da Karin Ajujuwa kayatattu a Makarantar Domin ganin Dukkan Daliban Makarantar sun koma kwana a cikin harabar Makarantar saboda amana ce gwamnatin da iyayen Daliban suka Basu .
Shugaban Rikon yaci gaba da cewa Gwamnatin zata Gina Benaye Guda biyu a cikin Makarantar Saboda ajiye dalibai maza da ayanzu Magoya yawan Daliban suke kwana a cikin gari maimakon kwana a cikin Harabar Makarantar wadda Samarda dakunan zai taimakawa Hukumar makarantar da su kansu iyayen Daliban wajan sanin tabbas na irin Rayuwar da yaran sukeyi .
Yakara da cewar gwamna Namadi Tasha alwashin Samarda sabon dakin kwaman Dalibai Mata saboda wadda suke kwana ayanzu ya Dauko lalacewa saboda hakane ma yasa gwamnatin tabada Umar in ahana Dalibai kwana acikinsa akokarin gwnati na Kare lafiyar Daliban Kuma akaba umarnin ahanzarta Gina sabon matsugunni ga dalibai Mata dake daukar darasi a kwalejin
Yace da zarar sun kammala Gina Sabbin Dakunan kwaman Daliban Hukumar Makaranta zatasanya Ido Akan Dukkan dalibai musamman dalibai mata babu 2ata Daliban da zata wuce large shida a wajan Makaranta Koda kuwa aranakun fitane Amma yanzu idan Daliban Bata cikin Makaranta babu yadda za ayi subasu cikakkiyar kulawar daya kamata alhalin kuma Amana ce iyayen da gwnati ta dankaasu .
A bangaran karancin Ajujuwa da suke damun Makarantar Na wani lokaci Mai tsawo acan baya yace yanzu Kam wahala ta Kare din gwna Namadi yasha alwashin share masu hawaye gwamnan Jihar yace Samar da Karin Ajujuwa saboda ya magance cinkosan dalibai a Ajujuwa Kuma za a gina gidajan Malamai a Harabar Makarantar da Nufin kyautatawa Malaman da iyalansu Suma su Sami Na tsuwa.
Haha zalika a bangaran Tsaro gwamnatin jahar tace zata inganta Tsaro a Makarantar ta hanyar samarda katafaroyar katanga da zata kewaye Makarantar Kuma za ta gina kofar Makarantar tayi saidai da kofofin Makarantu irin na zani Tareda Samarda Na,urorin aikin Tsaro da Karin ma aikatan Tsaro zakuma a samarda titi da zai Shiga cikin Makarantar tundaga Babban Titin Jahun zuwa Gujungu datake daf da kwalejin ya shiga cikin harabar Makarantar yayi kewaye a cikinta saboda zirga zirga ababen Hawa .
Abangaren kwalliya yakara da cewar gwnatin jihar zata Sanya manyan fitilun Kan Titi da zasu haskaka harabar Makarantar wadda hakan zai Taimaka wajan Samar da yanayin Tsaro Mai Nagarta a makarantar Kamar yadda yake a daukacin manyan Makarantu sake Fadin Kasarnan Shima anasa ran za ayisu daganan zuwa shekara Mai kamawa
Ganin yadda gwamnatin take kokari wajan Inganta Harkokin karatun kiwon Lafiya da Inganta Makarantar Nazarin kiwon Lafiya halayansa wakilinmu ya ziyarci kwalejin karatun Nazarin aikin Lafiya don ganewa idonsa halin da kwalejin take ciki
Abinciken dayayi ya gano akwai karancin masu Gadi da gwnatin ta Dauka take biyansu albashi saboda hakane ma ya tuntubi shugaban Rikon Makarantar akan matsalar yakuma shaidawa wakiliu cewar gwnati Yana bakin kokarinta wajan Ganin ta Kara yawan Jami an Tsaro da sukeyiba aiki a kwalejin din Ganin ankare rayuka da dukiyar Malamai da Daliban kwalejin .