Jihar Jigawa zata Samar da Wutar Lantarki Mai Hasken Rana a Asibitoci ,Makarantu da Gidajan Bada Ruwan sha

Jihar Jigawa dake Arewacin Najeriya ta fara daukar matakan dogaro da Kanta ta hanyar bunkasa Aikin gona da Samawa Kanta hasken wutar lantarki Mai Anfani da hasken Rana domin yanzu HaKa shirye shirye sunfara kankama na wadata Jihar dahasken wutar lantarki ta hanyar Anfani da hasken Rana ta hanyar Anfani da injina Sola Kamar yadda maibawa gwamna shawara ta fuskar makamashi Alhaji Hassan Usman Dakayyawa yafada awata zantawa dayayi da wakilinmu a ofishinsa

Sanin kowane Alh Hassan Tsohon Dan gwagwarmayane Kuma ayanzu HaKa shine Bulamai a garin Dakayyawa tun bayan rasuwar mahaifinsa Alh Usman saboda mutunne Mai Amana da gaaskiya yasa gwamnatin Badaru ta bashi mukamin maibada shawara Mai kulada fitilun Kan tituna na gyaransu a birnin Dutse wadda yanzu HaKa Kuma gwamna Malam Umar Namadi yasake bashi mukamin abangaran kulada hasken wutar abangaran Sola .

Inji saboda mashinmancin Sola Gwamnati zata maids Hankali wajanyin Anfani da injinan Sola saboda wadata Al,ummar Jihar da hasken wutar lantarki Mai Anfani da hasken Rana ,yace Gwamnati zata daina Anfani da injina masu Anfani Daman fetur da gas a daukacin asibitocin Jihar da makarantun kwana da tsangayun makarantun alloh saboda stage yawan kudaden da ake kashewa wajan Satan Mai MAIMAKON HaKa Gwamnati zatayi Anfani da kudin wajanyin mashinman Abubuwan more rayuwa dazasu taimaka wajan cigaban Rayuwar Al,ummar Jihar

Bulamai yakara dacewar yanzu wutar lantarki ta Nepa tayi ƙarancin Bata samuwa Dan HaKa yanzu shirye shirye yayi nisa wajan Samarda wuta Mai aiki da hasken Rana domin tuni gwamnatin Jahar Jigawa tayi Wata ganawa ta musamman da masana Sola a kasar amurka dazasu shigo Jahar domin farayin Aikin Samarda wuta Mai Anfani da Sola

Za,afara Samar da mega wort 100 ta wucin gadi da za arabawa asibitocin Jahar saboda kulada Marasa lafiya da Adana maganguna da nufin inganta harkokin kiwon Lafiya afadin Jihar

Yace yanzu hakama Mafiya yawan asibitocin Jihar suna anfanine da wutar Sola MAIMAKON Nepa musamman wurin ajiyar magani da dakunan Marasa lafiya

Yakuma bada tabbacin cewar dukkan asibitocin Jihar zasu komayin Anfani da wutar Sola MAIMAKON yin Anfani da wutar Nepa ,HaKa zalika Suma Cibiyoyin bada ruwansha dake Fadin Jihar ta Jigawa zasu komayin Anfani da injina Sola Dan tabbatar da cewar Jama a suna damun ruwansha akullum.kamar yadda gwamna yayi alkawri

Abangaran makarantun kwana na sakamdire Suma Gwamnati tayi kyaukyawan tanadi na Samarda wuta Mai Anfani da hasken Rana adaukacin makarantun Jahar musamman makarantun kwana na maza da Mata

Yaci gabada cewar makarantun tsangayama Gwamnati tayi masu tanadin hadasu da hasken wutar Sola tareda hada rijiyoyinsu na ruwa da hasken Sola domin ganin daliban makarantun Jihar sun Sami karatu cikin natsuwa kasancewar su dama dare lokacin yin karatun tilawa awajansu .

Daya juya wajan batun harkar Noman Rani kuwa cewa yayi Gwamnati ta sayi injinan noman Rani masu aiki da Sola wato hasken rana domin Rabawa manoman Alkama Dana shinkafa afadin Jihar ta Jigawa

Yaci gabada cewar yanzu HaKa wurin Adana Kaya wato store na kamfanin Aikin gona na Kasco makare take da injinan Sola da Gwamnati ta shigo dasu domin Rabawa manoma afadin Jihar ta Jigawa Mai kananan hukumomi 27

Dan HaKa Bulamai ya Gargadi manoma su baiwa injinansu kulawa domin injinane masu tsada Kuma duk Sola panel yanada lamba a jikinsa don HaKa duk wadda aka Kama da injina Sola kopel dababu risiti na satane Gwamnati zata Sanya idanu akan barayin injinan Sola Kuma duk wadda aka Kama dashi shine barawon.

Ya nuna damuwarsa akan yadda barayin wayoyin wutar lantarki suke sace some da armo cable a rijiyoyin Samarda ruwansha saboda hakane ya shawarci Manoman su Sanya Ido akan kayanda za abasu

Bulamai yace duk wadda suka Kama da kayan Sola Bazasu kyaleshiba komai matsayinsa zasu gurfanar dashine agaban kuliya domin ayimar hukuncin Daya dace dashi domin hakan ya Zama darasi gana baya masu irin halinda .

Awake Daya Kuma ya hori Yan Kasuwar masu harkar Sola su Rika baiwa duk wadda ya sayi kayansu risiti saboda duk wadda suka Kama Yana Anfani da Sola agonarsa Babu risiti matukar Babu Wata Shaida data nuna saya yayi barawone saboda HaKa hukuma zata cafkeshi

Yakarada cewar ofishinsa zaiyi Anfani da Jami an tsaro wajan Kama barayin Sola da zasu kawowa Gwamnati cikas akarkashin Shirin Dan HaKa Gwamnati tayi tanadin Daya kamata ta Hana masu satar Sola da kayan Sola afadin Jihar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here