Kungiyar Tajadidil Islam Ba Tada Alaka Da Siyasa Hidima Take Wa Addinin Allah

Kungiyar Tajadidil Islam Ba tada wata alaka da siyasa kungiya ce mai zaman kanta da take yi wa addinin Islam hidima aikin da har kullum shi ne horo da aiki mai kyau da hani da mummunan aiki. Kamar yadda Shugaban kungiyar na kasa Reshen Jihar Jigawa Alh Ismaila Ahmed Kudai ya shaida wa Jaridar Mizani a wata tattaunawa da suka yi a ranar Juuma’ar da ta gabata.

Kudai ya ce yana daga cikin kyawawan manufofin kungiyar a yada Da’awa da tallafawa marayu, gyaran masallatai da gina masallatai da samar da makarantun islamiyya. Da kuma gina tuka-tuka a yankunan karkara da nufin inganta ayyukan ibada a kauyuka a Nijeriya.

Ya cigaba da cewa yanzu haka akwai shirye-shirye da suke yi na inganta rayuwar marayu wadda tuni suka dauki sunayen marayun suka tura babban ofishinsu domin ganin an bada taimakon da yakamata a kansu.

Da ya juya wajen ayyukan masallatai da Kungiyar Tajadidil Islam take yi yanzu haka a Jihar ta Jigawa ya ce aiki ya yi Nisa wajen gina masallatai takwas na kamsas-salawati masu fadin mita takwas da makewayi da fanfunan alwala.

A kauyukan Jigawar Auduwa ,Masanawa, Kudai ,Dutse Shafa,Sabuwar Unguwa,Katangar Lafiya,Zunzala,da Kuma shirin gina masallatai na Juma’a nan gaba.

Kudai Ya kuma bukaci Gwamnati da ya shigo ta taimaka wajen gina kananan masallatai da mutane suke bukata a gina musu wadanda ba su kai girman wadanda suke ginawa ba. Ya ce a shirye suke su bai wa Gwamnati hadin Kai wajen ba su sunayen kauyukan da suke da bukatar a ginae musu irin wadancan masallatai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here