Dutse Matukar akaci gaba da tafiya akan halinda ake ciki yanzu a Nigeria daga nan zuwa shekaru goma shabiyar musamman a Arewa akwai Rashin tabbas na samun rayuwa mai inganci awajan yan Nigeria
Jawabin hakan ya fitone daga bakin jagoran kungiyar Sawaba ta kasa wato Sawaba initiative for humanitarian development Alh Umar Dan jani a wajan wani taro da kungiyar ta Kira a dakin taro na Hanan hang out dake Dutse shedikwatar jihar jigawa aranar asabar din nan .
Ya aiki lamirin yadda shugabannin siyasa suka sace kudin kasa sukabar al umma cikin kangin fatara da talauchi saboda haka dole sai jama ar kasa sun san kansu sun tsaya staying daka wajan kare hakkinsu wajan tsayawa su fadawa shugabanni gaski.
Yace yazama dole su saitasu matukar basuyi hakaba za ayita fuskantar matsala matar iyaka a Najeriya
Ya kuma nuna damuwarsa yayinda aka wato gari almajirai akabarsu da yunwa da fatara kuma za a wayi gari almajirai basuda ilimi babu aikinyi kuma duk abubuwa daya kamata ayi masu ya garaga samuwa jama a na iya samun kansu cikin katuwar matsala .
Saboda wadansu matasan kishin kasa barayi sunyi samara da fadi da kudin jama a hakan zai iya jefa kasar cikin wani halin kuncin rayuwa wadda hakan yasani tausayin kaima da sauran jama ar Nigeria inji komarade dan jani.
Jagora tafiyar na kasa wato Alh Umar Dan jani yace sunkafa kungiyar Sawaba ne domin ganin an ceto rayuwar talakawa daga mawiyacin halin rayuwar da jama a Suka Sami kansu a ciki.
Yakarada cewar ba dadi bane ,ba Murna bace tasa Suka kafa kungiyar ta Sawaba masifa ce da Suka hango da bala,I daya tinkaro Nigeria musamman arewa cin Nigeria saboda haka ne Suka yanke shawarar kafa ita wanna kungiyar ta sawaba domin tinkarar duk wani kalubale daka iya zama cikas ga rayuwar al Umar Nigeria da nufin baiwa al,umma kariya.
Yakarada cewar kungiyar Sawaba a baya ta aiwatar da aiyukantaba wajan ceto rayuwar jama,a ,itama Sawaba ayau saida ta Sami cikakkiyar damage yin rijista da gwamnatin tarayya kuma tuni suka sanarda dukkan ofisoshin jani an tsaro amatakai daban daban yadda kungiyar zataci aiki wajan kwato hakkin talakawa
Yaci gaba da cewar anjima anayin kungiyoyi iri daban daban a Nigeria Amma mafiya yawansu kungiyoyine na yan danfara yayin da wasu da. Dama kuma suka kasance kungiyoyine na sankai bana sakaiba saboda hakane yasa da suka kafa kungiyar Sawaba sukace bazasuyi anfani da sunan coordinator ba sai suka Kira shugaban wannan kungiyar da sunana president kuma amatakan jihohi sunada gwamnoni a matakan kananan hukumomi kuma sunada ciyamomi Kamar yadda yake a tsarin gwamnatin kasa .
Dan jani ya kara dacewar sun shirya tsaf zasuyi Rigima marar iyaka Kamar yadda iyayen su sukayi wajan kwatowa talakawa hakkinsu da cetosu daga masifa iri ,iri a shekarun baya lokacin talaka bai Isa ya motsa baki ko tsoma bakinsa a harkar mulkin kasar nanba.
Wadda a wancan lokacin talaka bai Isa ya tsaya takaraba azabeshi harsaida jam iyar nepu ta jajirce talakawa suka Sami bakin magana ,atakaice ita jam iyar Nepu itace fitilar talakawa a wancan lokacin.
Yakuma kalubalenci daukacin malaman addini na Najeriya dacewar Sunada hannu dumu dumu wajan Russ tattalin arzikin Najeriya yace malaman da yake nufi dune malaman dukkan bangarorin biyu wato malaman musulunci da majama,u ma,ana musulmi da kirista.
Yakara dacewar musulmi zai sace kudin kasa mai makon malaman addini subada goyan baya a hukuntashi sai suje har gida suna kai Masa ziyara tareda yimasa adduoi yayin da suma kiristocin Najeriya idan kirista ya sace dukiyar kasa zakaga wannan barawon Yana ziyara coci majamiun coci sunayimar addua .
Dan jani yakara dacewar babu ruwan yunwa ko talauchi da banbancin addini domin mafiya yawan shugabanni Nijeriya suna anfanida jahilci tare da Talauchin yan Nigeriaya ne suna sace dukiyar kasa ko kudin daya kamata ace mutane militant biyu sun anfana sai mutun gonna kachal su handame saboda kwadayi da son zuciya irin na shugabanni marasa kishin kasa.
Yakumayi bara zanar cewar lokaci yayi da dukkan yan Najeriya xasu fito su daina nade hannu suna kallon wasu yan siyasa marasa kishin kasa suna karkatar da dukiyar kasa ta barauniyar hanya,yakara dacewar bazasu bari a Rusa rayuwar yara masu tasowa nan gaba ba .
Yaci gaba da cewar a shirye suke da duk wani kalubale wajan kare muradin yan Najeriya musamman barayi masu sace kudin yan Najeriya kungiyar Sawaba zata sanya kafar wando daya ga daukacin dukkan Bata gari da suka hana ruwa gudu a farin Najeriya .
Yakara da cewar yan kungiyarsu dake daukacin kananan hukumomi afadin Najeriya zasusa Ido akan kudin da gwamnatin tarayya take turawa kananan hukumomi gwamnatin jihohi domin domin sabin yadda ake kashesu ..
Kwamared dan jani yakara da cewar zasuci gaba da shirya gangamin wayarda kan al imma akai akai domin al umma Susan kansu kuma Susan nawa gwamnatin tarayya take baiwa jihohi da kananan hukumomi su kuma su rikabin dididigin yadda ake kashe kudaden
Yakara da cewar Sawaba zataci gabada bayar gudun mawarta wajan taimakawa makarantun primary dana sakandire wajan ganin yayan talakawa sun Sami ilimin daya kamata ace sun Samu Kamar yayan kowa a Najeriya.
Yakuma tabbatar da cewar zasu saka wando kafa daya da mutane da ake Basu aiki amatsayin yan kwangila kuma basayin aiki mai nagarta ko kuma ake had baki dasu ake sace dukiyar gwamnati alhalin basuyi aikinba