Shugaban Hukumar Tsaro Ya Ajiye Aiki Kan Zargin Alaka da ‘Yan Bindiga Daga Nada Shi

Jim kadan bayan Rantsar da shi a matsayin shugaban kwamitin da zai kafa jami’an tsaron sa kai, Garba Moyi Isa ya yi murabus. Kamar yadda Jaridar Legit Hausa ya wallafa a shafinta na internet .

Jaridar ta legits hausa race ta Sami labaran be daga jaridar Leadership hausa cewa Kanal Garba Moyi Isa mai Ritaya ya sauka daga kujerarsa da gwamnatin jihar Sokoto ta nemi dora shi.

Garba Moyi Isa ya yi murabus ne bayan ‘yan awanni da rantsar da kwamitinsa mai mutum 25 a yunkurin neman kawo zaman lafiya a yankin Sokoto.

Ana tunani tsohon sojan ya dauki wannan mataki ne saboda wani bidiyo da aka fitar, ana zargin ya na da alaka da ‘yan ta’addan da ke Sokoto.

Garba Moyi wanda ya Rike kujerar Kwamishina har sau uku a jihar Sokoto, ya tara manema labarai a karshen makon jiya, ya yi jawabi.

Tsohon jami’in tsaron ya yi bayanin yadda ya bautawa kasarsa na shekara da shekaru a gidan soja, daga baya kuma ya shigo siyasa.

Koda yake duk do gon jawabin dayayiwa manema labarai Moyi Mai Ritaya Bai fadawa duniya dalilan sa na ajiye mukaminba Kamar yadda Jaridar punch ta bayyana a shafin ta na internet

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here