Wasu Mafarauta a kauyan Tage Sun Damƙe Ɗan Fashi a Jigawa

Wasu Mafarauta Mazauna kauyen Tage da ke karamar hukumar Kafin Hausa a Jihar Jigawa a ranar Litinin din da ta gabata, sunyi artabu da wasu gungun ƴan fashi,da makami yayin da sukayi gaba da gaba dasu, akan hanyar su ta zuwa Hadejia.

Wannan turjiya da suka yi da Yanfashine ya kai ga cafke daya daga cikin ‘yan ta’addan yayin da wasu kuma suka yi ta ɗauki-ba-daɗi da sauran bayan da suka Sami Nasara suka arce.

Wani ganau da lamarin ya faru agansa ya zanta da manema labarai ya bayyana cewa al’ummar yankin sun yi wa daya daga cikin ‘yan fashin ƙofar rago, kuma suka ji masa wani wawan rauni, ta hanyar yanka da wuƙa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa, DSP. Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da cewa sun samu labarin cewa wasu gungun ‘yan fashi da makami sun tare hanyar Tage zuwa babbar hanyar Hadejia tare da yi wa mutane fashi da makami.

Adam ya kara da cewa an tattaro ‘yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru, “sun gano cewa wasu gungun mutane ne suka taru suka fuskanci barayin, a sakamakon haka sun yi wa daya daga cikin ‘yan fashin mai suna Abdullahi Abubakar dan kauyen Hago, wani wawan rauni

Kakakin ya ce ‘yan sandan sun ceto dan fashin da ya samu rauni tare da kai shi babban asibitin Kafin Hausa domin yi masa magani.

Ya ce an kwato alburusai da kuma kudi naira dubu talatin da bakwai (N37,000.00k) daga hannun wanda ake zargin.

Hakazalika Adamu ya tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike don kamo sauran wadanda ake zargin da suka cika rigarsu da iska wadda yanzu haka yansanda me nemansu ruwa a jallo

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here