Wasu Mutane daba asan suwayeba daukeda manyan bindigogi akan Babura sun Kai Hari kauyan Atawame sun sace Dagacin Atawame Alh Abdullahi Atawame Mahaifin Shugaban Asibitin gwamnatin Tarayya na birnin kudu Alhaji Adamu Abdu Atawame .
Yan bindigar sunje kauyan Atawame ne da misalin large Daya da rabi na Daren Ranar Litinin wayewar garin talata suka sace tsohon Bayan sun toshe dukkan kofofin shiga garin da matasa dauke da Manyan bindigogi sun Hana kowa ficewa daga kauyen.
Kakakin Rundunar Jami an tsaro ta farin Kaya da Hana fasa bututun Mai ta civil defense Sp Adamu shehu ya tabbatar da faruwar labarin yace alokacin da wasu Yan uwan wadda aka sacedin suka Sanarda Shi domin Neman agajin Jami an tsaro karfe Daya da minti ashirin na dare .
Yaci gaba da cewar barayin Saida sukayi tafiyar kilo mita shida akasa kafin suje inda suka ajiye baburansu kafin su there dashi zuwa wata maboya wadda Babu Wanda yasani .
Yakara dacewar ansaki tsohon a Jiya Alhamis bayan sallar magariba bayan sun ajeyeshi wani wuri nesa da kauyansu Kuma suka sanar da Yan uwanka cewar sune zasu sameshi awurin Amma tsohon Bai Isa gidansaba sai wajan karfe Tara na dare .
Yaci gaba da cewar a lokacin da barayin suka sace tsohon Yana Famada matsalar ciwon kafa bamaya iya tafiya da Sanda take dogarawa watakila hakan yanada nasaba da dalilin dayasa barayin suka sakeshi
Nayi iya kokarin jinta bakin Adamu Abdu Atawame wato Dan Dagacin na Atawame Amma hakan yaci tura saboda wayarsa Bata Shiga domin jin konawa Yan Bindiga suka bukata awajansa amatsayin kudin fansa kafin su saki Mahaifin nasa Amma bansami ikon yin magana dashiba
Hakan zalika na tuntubi kakakin Rundunar yansanda na Jahar Jigawa Lawan shisu Adam akan sahihancin labarin yakada Baki yace Basu da masaniya akan labarin Amma zasu bincika Kuma zai sanardamu halin da ake ciki insun kammala Bincike .
Har zuwa lokacin da muke tattara rahotanmu Bai kiramuba