Rikichin Fulani da Manoma Al,amarine daya jima Yana chima Manoma da Fulani makiyaya tuwo akwarya a yankin karamar Hukumar kiri kasamma da kewaye tsawon shekarun Masu Yawa .
A iya cewa hakan ya jima Yana faruwane saboda Rashin kulawar shugabanni awancan lokaci tsawon shekarun da suka Gabata abaya
Yanzu kam ana iya cewa Maganar Rikichin Manoma da Makiyaya Al amarine da yazama sai tarishi babu sauran Rikichi tsakanin bangarorin biyu wato Manoma da Makiyaya.
Hakan ya biyu bayan irin matakan da gwamnatin Jihar Jigawa ta Dauka karkashin ikon Malam Umar Namadi a Matsayin sa na Gwamnan Jihar Jigawa wajan aiwatar da sasanto a tsakanin bangarorin biyu
A lokacin da gwamna Umar Namadi ya kafa kwamatoci akowanne bangare domin yiwa ko wanna bangare Adalci kuma sukeyin aiki tareda Juna danganin ba a sake samun wata baraka ba
Haka ya baiwa shugaban karamar Hukumar kiri Kasamma damar kafa kananan kwamatoci a kauyuka a daukacin mazabu goma da karamar Hukumar take dasu wadda sukeyin aiki tareda babban kwamatin Jihar domin ganin an Sami Nasara wajan Murkushe duk wadanda suke kokarin tayar da hargitsi a yankin
Wakilinmu ya ziyarci yankin karamar Hukumar kiri Kasamma yakuma zanta da shugaban karamar Hukumar Alh Isah Adamu matara ya kuma shaidamar cewar Rabon Asamu zaman lafiya a yankin anjima tsawon shekaru Masu yawa Sai da gwamna Malam Umar Namadi yazamo gwamnan Jihar jigawa ya kafa wannan kwamatin.
Dan haka acewarsa babu gwarzo daya dace ayiwa jinjina Kamar gwamna Umar Namadi wajan kokarin wanzar da zaman lafiya idan aka Kira Namadi da kimanin zaman lafiya ya chanchanta domin yayi kokarin inji matara
Yace tunda yakafa wannan kwamatin babu sauran tashin hankali ayankin kiri Kasamma, Guri da Birniwa saboda da Magance Rigima ta Rashin hankali tun kafin takaiga lalacewa anyi maganinta .
Abangaran aiyuka karamar Hukumar ta kiri Kasamma ta Gina manya da kananan asibitoci kusan guda goma Masu gadajan kwanciya guda goma tareda daukar malaman kiwon lafiya na wucin Fadi mutun 45 a kokarin karamar Hukumar na inganta kiwon lafiya .
Yace mutane 45 da suka dauka aikin kiwon lafiyar zasuyi aiki tare da ma aikatan lafiya na gwamnati wajan ganin ankaiga samun nasara wajan baiwa marasa lafiya kulawar da suke bukata.
Matara ya karada cewar shi babu abinda yakemar dadi a ransa irin samun cikakken zamani lafiya ayankin da ya Zama babu sauran batun maganar Rikichi ko Rashin hankali tsakanin manoma da makiyaya ayankin na kiri Kasamma
Matara yace ya godewa Allah daya kawo karshen matsalar Rashin tsaro ayankin wadda hakan yafarune tareda kokarin gwamnatin Jihar Jigawa karkashin kulawar gwamna Umar Namadi fca