ZAN MAYARDA HANKALI WAJAN INGANTA RAYUWAR MUTANEN KARKARA….Tasi,u Ishaq Soja

Dan majalissa Mai wakiltar Karamar Hukumar Dutse a Majalissar Dokokin Jihar Jigawa Alh Tasiu Ishaq Soja Dutse ya bukachi Al,ummar Jihar Jigawa su baiwa gwamnati hadin kai wajan aiwatar da aiyukan alkairi da gwamnatin keyi

Alh Tasiu yace a tarishin duniya Babu inda gwamnati take samun ci gaba Saida hadin Kan Al,umma ,Don haka ya Zama Dole a hadu amarawa sabuwar gwamnati Mai zuwa baya Kamar yadda aka marawa gwamnati maichi yin hakan zai taimaka wajan yiwa Al,umma aiyukan Al,kairi

Soja ya hori yayan jam,iyar su na apc su guji yada jita jita da kokarin kunna wutar fitina da zata Zama matsala a cikin jam,iyar da ita Kanta gwamnati ,yace yin hakan bazai haifar da alkairi ba .

Dan haka ya hori yayan jam,iyar dasu hadakai wajan marawa gwamnati Mai zuwa baya Kamar yadda suka baiwa gwamna Badaru goyan baya kasancewa da gwamna Badaru da malam Umar Namaddi Dan jumane da Dan jumai ,yace yin hakan zai taimaka gwamnati ta Sami damar cika alkawiran da aka dauka lokacin yakin Neman zabe .

Yaci gabada cewar Rarrabuwar Kai bata iyakai Al,umma ko Ina sai koma baya Dan haka hadakan Al,umma lamarine Mai mashinmancin gaske ,musamman a fagen siyasa .

Yakara da cewar “Ni awajena Dan jam,iyata ta apc a Enugu Dan uwanane bashida banbanci da Dan uwana na jam,iyar apc dayake Jahar Jigawa ,saboda haka duk Dan jam,iyar apc a duk inda yake bashida banbanci a wajena dukansu matsayinsu dayane awurina ” inji soja .

Duk wani rikici da wasu marasa kishin jam iyarmu suke kokarin haifarwa bazaiyi tadiriba saboda shugabannin mu kwararrune sunsan siyasa bazasu Bari asami wata matsala ba a cikin jam,iyarba Ina tabbatarma za a sasanta Kuma za ,a a magance dukkan wata matsala

Daya Juya wajan batun Rayuwa da tallafawa Jama a cewa yayi bashida wani buri Daya wuce yaga ya kyautatawa Rayuwar Al ummarsa musamman mazauna yankunan karkara.

Yakara da cewar shifa bashida wani buri aransa Daya wuce ya inganta Rayuwar Al,ummar masarautar Dutse ,Ni tunkafin na shiga siyasa dama banida aikin Daya wuce na inganta Rayuwar Al umma musamman mazauna karkara ta hanyar Basu ilimi ,ruwansha da inganta lafiyarsu

Saboda haka da zarar na shiga majalissa amatsayin Dan majalissa Mai wakiltar Karamar Hukumar Dutse a sauran majalissa Zan tsaya kaida fata wajan Samar da ilimi kyauta ,ruwansha da kiwan Lafiya acikin aiyukan da gwamnati takebawa Yan majalissa dama suyi

Soja yakarada cewar tun kafin ya tsunduma cikin harkokin siyasa yanada gidauniya dayake ANFANI da ita wajan inganta Rayuwar Al,umma

“Inada gidauniya ta da ake cewa G 7 da Kuma gidauniya ta soja Riga Riga Ina ANFANI da ita wajan inganta Rayuwar Al,umma Dan haka ko yanzu zanci gabada ANFANI da ita wajan taimakawa dukkan Al umma da kudadena danake kasuwanci da nakafata da dukiyata Babu maganar siyasa a cikinta .

Hakan zalika zanyi ANFANI da ita gidauniyar wajan aiwatar da aiyukan Raya kasa ga Al ummar Dutse da kewaye .

Kuma zanyi iyakacin bakin kokarina wajan samawa matasa aiyukanyi ta fuskar samarda kanfanoni wadanda zasu taimaka wajan rage yawaitar matasa marasa aikinyi a Karamar Hukumar Dutse .

Saboda yanzu haka akwai wasu abokaina da gwamnatin Jigawa ta Basu filaye zasu Gina kanfanoni anan Babban birin Jahar Kuma da zarar sun kammala zasu dauki matasa masu yawa aikinda zasu dogara da kansu

Haka zalika nikaina inanan Ina kokarin Gina kanfanin Taki wadda zai taimakawa manoma wajan samun Taki Mai Nagarta sukuma matasa zasu Sami hanyar dogaro dakansu.

Abangaran inganta Rayuwar mutanen karkara zanyi iyakacin kokarina wajan samarda ruwansha da ilimi da kiwan Lafiya da zarar na shiga majalissa saboda wadannan sune Rayuwar Dan Adam .

Abangaran zai zayar kasa data Jima Tana addabar mazauna Dutse da kewaye yace gwamnatin Jihar Jigawa Tana iyakacin bakin kokarinta wajan magance matsalar domin tuni gwamna Badaru ya sanarda gwamnatin tarayya irin halinda masarautar Dutse take ciki harma Masana sunfara aiyuka wajan kawo karshen matsalar afadin Jahar ta Jigawa

Yakuma yabawa gwamnatin Alh Badaru Abubakar akan kokarin dayakeyi na kawata Babban birnin Jahar Jigawa Dutse ta fuskar Gina manyan kofofin gari na tarishi da wurin shakatawa inganta fitulun Kan titi wadda gwamnati ta ware makudan kudade masu yawa domin Aikin

Yakara da cewa Shima gwamna Dan modi mutunne Mai kishi Kuma Yana rikon Amana da addini yace ya tabbatar zai karasa dukkan aiyukan da gwamna Badaru Bai kammalaba Kuma ya Dora da sabo daga inda ya dakata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here