Daga Nasir Muhammad AbbasGaskiya da amana ya sa talakawan Nijeriya suke yi wa Gwamnan Jihar Borno jinjinar giramawa, ba wai don ya fi sauran gwamnoni ba.
A duk fadin Nijeriya shi kadai ne gwamnan da ya yadda akwai Allah Ya kuma yadda akwai kaddara kuma yake tare da jama’arsa tsakaninsa da Allah. Kuma yake son talakawansa tsakaninsa da Allah yake kishinsu don Allah. Ba ya san yaga wata damuwa ta samesu.
Zulum ne ya ciri tuta a cikin jerin gwamnonin Nijeriya duk runtsi yana tare da talakawa. Duk inda aka ce akwai matsalar tsaro ba ya gagara yajve ya ga halin da talakawansa suke ciki. Haka ya sa talakawan Borno da ‘Yan Nijeriya suke kaunarsa. Zulum ya fita zakka a cikin shugabanin Nijeriya.
Na yii imani duk lokacin da aka ce ya sami wata dama ya zama Shugaban kasa a Nijeriya zai gyara Nijeriya domin yana da kishi.Yana kaunar ‘yan Nijeriya, ba ya son ya ga damuwa a fuskokinsu.
Tun kafin gwamnatin tarayya ta yi tunanin taimaka wa talakawa da abinci da gyara makarantu da inganta harkar lafiya da gyara hanyoyin mota Zulum yake wa talakawa aiki a Borno.
Duk Nijeriya gwamna Zulum ne bai cuci talakawansa ba wajen raba tallafin kayan abinci da aka ce a raba ea ‘yan Naieriya.Saboda ya yi rabon kayan abincin babu nuna kabilanci ko addini ko kuma bambancin siyasa. Duk Magidanci an ba shi kayan abinci a wadace ba kamar yadda wasu suka rika raba buhu ashirin a mazaba ba, mai mutane sama da dari biyar (500). Wa za a baiwa, wa za a hana?
Duk da gwamna Zulum ba gwamnan jahata ba ne ya cancanci a yaba masa domin yana da tausayi bai zama cinye-du-ba. Amma wasu gwamnonin a Arewa ba su da aiki kullum sai yawo a titi tsakanin Abuja zuwa jiharsu da sunan wai za su nemo wa jiharsu abubuuwan more rayuwa.
Bangaren siyasa kuwa Gwamnan Jihar Lagos Babajide Sanwolu na cira masa hula saboda shi kadai ne gwamnan da ya nuna yana da kishin wadanda suka taimakeshi a lokacin yakin neman zabe. Kuma yake saka masu da abubuwan alkairi.
Domin kusan kashi tamanin (80%) na mutanen da suka ba shi gudunmawa a siyasa ta kudi ko ta aiki ko waka ya biya su da hanyar da yakaamata ya sakama su.
Shi ne gwamnan da aka cusa masa sunayen wasu ‘yan PDP a matsayin kwamishinonin da zai nada, ya yi fatali da su ya ce a Fada masa gudunmmuwar da suka ba shi saboda haka ba zai nada su ba.
Amma a wasu jihohin a nan Arewa muun sani wasu ma suna can suna sassakar turmi a daji, kuma ba su yi APC ba haka aka debo su aka ba su mukamai. Wasu ma sun zame mana barazana a lokacin yakin neman zabe saboda kawai ba sa jin dadi. Amma an kira su an ba su matsayi. Yanzu su ne ‘ya’yan Mowa, mu kuma an mayar da mu ‘ya’yan Bora.
Da a ce ba a sauya wa gwamnonin tunani ba ta hanyar tsafi da shirka ba, na tabbatar da sun yi abinda yakamata. Amma saboda ni a yadda na fashinci tsarin siyasa duk wadda ya yi tsakaninsa da Allah ba kasafai yake cin moriyarta ba. Kuma wadda yake mata kaluluwa shi ne yake morarta.