Jami an tsaro sun hana yan majalissar dokokin shiga fadar Dutse wajan Nadin Sardauna

Jami an tsaro na farin Kaya sun hana shugaban Masu Rinjaye a majalissar dokokin ta Jihar jigawa Alh Lawan Muhd Dan,sure shiga fadar Mai Martabar sarkin Dutse a lokacin bikin nadin Sardaunan Dutse Alh Nasiru Haladu Dano wadda ya gaji kujerar Alh Bello Maitama yusuf Tsohon sardaunan Dutse wadda ya Rasu a shekarar data Gabata

Jami an Tsaron sanye da bakaken gilasai sun Sami damar korar shugaban Masu Rinjaye da tawagarsa a lokacin da suka halacci fadar ta Mai martaba Sarkin na Dutse Alh Hamim Muhd sunusi a lokacin daya Kaddamar da nadin Alh Nasiru Haladu Dano a Matsayin sabon Sardauna Dutse

Hana shugaban Masu Rinjayen shiga fadar ya batawa mutane da dama Rai Matuka ciki harda sauran yan majalissar dake cikin tawagarsa da sauran jama a dasuke kofar shiga wurin da ake Gudanar da Nadin , lamarin dayasa yan majalissar suka fiche daga fadar cikin fushi suka hau dovuwar motarsu suka fice daga fadar suka koma inda suka fito .

Daga cikin wadanda suka rufawa shugaban Masu Rinjayen Baya a majalissar jihar Baya sun hada da Alh Aminu sule Sankara da yahaya muhd maliya da Ilu Maku Garki da Ibrahim Hamish kanya da Aminu Zakari Tsubut a lokacin da suka rufawa Alh lawan Muhd Dansure Baya domin zuwa fadar domin ganin yadda Nadin yake Gudana

Jami an Tsaron Basu tsaya iyakan yan majalissar ba hatta sakataren mai martaba sarkin Alh wada Alh bai tsiraba Saida sukayi iya kokarinsu wajan hana sakataren shiga fadar wurin da ake Gudanar da Nadin Saida wasu Manema labarai suka gaya Masu cewa shine sakataren sarkifa sannan suka barshi ya shiga saboda basu sanshi ba.

yayinda yan jaridu da dama katin shaidarsu baiyi Masu Anfani ba wajan shigar fadar inda akeyiba bikin nadin domin Jami an Tsaron sunki barinsu su shiga wurinda ake bikini nadin sai a jikin katanga suka makale tamkar kadangaru Suna leketa tags tamkar mabarata

Yayinda mutane da dama ciki harda wasu daga cikin shugabannin kananan hukumomi Basu Sami ikon shiga dakin taron ba saboda Barazanar Jami an tsaro da kaicewa cin zarafin su yayinda mawaka da dogarai da makada akayi fatali dasu gefe daya aka hanasu shiga suma.

Abangare daya kuma yan sane ne sukaci karensu babu babbaka wajan sanyawa mutane Hannu a aljihu suna dauke Masu yan kudade da waypyin Hannu a lokacin fitowa da lokacin shiga wajan taron Nadin saboda kokawa

Duk da hakaTaron Nadin yasami halartar tsohon shugaban kasa Janar Muhd buhari da Mataimakin shugaban kasa kashim shatima da janar burtai da sanatoci da manya ministocin kasar nan harma da baki daga kasashen waje

Anyiwa fadar ta Dutse kwalliya ta musamman saboda da gagarimin Nadin yayinda kowa ka duba afada da kewaye Yana cikin farin ciki saboda yadda bikin ya kayatar .

Dutse tayi cikar kwari data jima batayiba domin Rabon aga taro irin wannan tinkafin easiest tsohon sarki kuma an shiryawa Dano gagarimar liyafa afadar gwnatin Jihar Jigawa Jim kadan bayan kammala bikin nadin abin sai wadda yagani

yayinda aka shirya gagarimar Dinna ta musamman adaren Ranar larabar data Gabata kafin bikin nadin domin nunawa wadda akayiwa Nadin cewa gwamnati tana taredashi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here