Karancin Kayan aiki ya addabi Makarantun Jihar Jigawa

Dutse Karan cin Kayan koyarwa ya addabi Makarantu da malamai a Jihar Jigawa lamarin dayasa wasu daga cikin malaman makarantun Jihar gabatar da korafin su ga Manema labarai

Kadan daga cikin korafin ya hada da karancin Alli da rijistar dalibai da scheme of work da kuma karancin littatafan koyarwa a makarantun .

Yayin da a wasu bangaren kuma malaman sukayi korafin Rashin kulawa akansu wajan Karin girma da gazawar gwamnati wajan biyansu hakkinsu na Karin girma Akan lokaci

Dayawa daga cikin Masu korafin sun bukaci sakaya sunansu saboda wasu malamai kuma sun karada da cewa dayawa daga cikinsu da aka kara Masu matsayi har yanzu albashinsu bai sauyaba ga girma a takarda Amma babushi a aikace

Saboda haka sun bukaci gwamnatin Jihar Jigawa ta duba matsalarsu sukace Amma maimakon ace gwamnatin tana kulada hakkinsu saima kara Masu matsaloli takeyi akansu

Sun koka Akan cewar An shigo da Wani sabon tsari na cewa malamai dole su koma Makarantu kafin dawowar dalibai da sati daya alhalin ita kuma gwamnatin Bata kula da hakkin malaman kamar yadda su malaman sukayi korafin

Dayake mayarda jawabin sa babban sakataren a Hukumar ilimi matakin farko farfesa Haruna Musa yace tabbas akwai matsala ta karancin Kayan aiki a makarantun Amma tuni ma aikatar ilimi ta samarda Alli a daukacin makarantun kuma an ware wasu makudan kudade wadda tuni gwamnatin ta sakesu domin sayan Kayan karatu ga daukacin makarantun domin ganin ankawo karshen waccan matsalar .

Daya juya wajan batun Karin girman malamai da wasu suke korafin yace gwamnati zata duba matsalar kuma Duk wadda ya chanchanta akaramar girma za a karamar zuwa matakin daya dace .

Yakuma karada cewar wata katuwar matsala da suke Fuskanta shine bayan ankarawa malaman girma a kananan hukumomin da suke aikinsu na koyarwa sai akasa biyansu albashin daya kamata abiyasu .

Yakara da cewar zasuyi iyakacin bakin kokarinsu wajan ganin Duk malaman da aka karawa girman kananan hukumomin sun Sanya albashinsu Akan matakin albashin da aka dorasu.

Saboda haka ya Umarchi iyayen yara dasu rika mayarda yaransu zuwa Makarantu Akan lokacin da gwamnati ta shinfida ,yace gwamnati ta fito da Tsarin hakane da nufin ta inganta harkokin ilimi a fadin Jihar .

Yakara da cewar shirin bashaida wata matsala a cikinsa ba kamar yadda malaman da suke korafin suka fashinta ba yace shirin yanada kyau domin shida kansa ya ziyarci makarantun Jihar Akan yadda shirin ya Sami karbuwa kuma anfara samun zaiyi akan yadda harkokin karatu yake tafiya a daukacin makarantun Jihar .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here