Karancin Motocin Daukar Kayan ya Addabi Hukumar SEMA ta Jihar Jigawa

Gobara ta shafe kayayyaki na kimanin Naira miliyan Arbain a Jihar Jigawa Sakamakon Yawan Tashin Gobarar babu kakkautawa a Jihar kamar yadda shugaban Hukumar sema na Jihar ya Shaidawa Manema labarai Alhaji Haruna Mai Riga .

Babban sakatare a Hukumar bada agajin Gaggawa ta jihar Jigawa SEMA Alh Haruna Mai Riga yace akwanan Baya Gobarar Ta chinye Runbuna Maganin Gona masu Yawan gaske a kauyan kwalele dake karamar Hukumar buji wadda aka kiyasta hasarar kudin yakai Naira miliyan Ashirin da biyar

Haka zalika yace Wata Gobarar ta tashi a makarantar kwana ta Sakandire dake Aujara a karamar Hukumar Jahun wadda tayi sanadin konewar a kwatinan Kayan dalibai da katihun kwana dalibai a wurin ajiye Kayan dalibai dake makarantar shima anyimasa kiyasi hasarar da Gobarar ta haifar yakai Naira Miliyan goma Sha biyar

Mai Riga yaci Gaba da cewar wata Gobarar kuma ta Tashi A makarantar kwana ta yan,mata ta gwamnatin tarayya dake kazaure itama ta kone Kayan kwanciyar dalibai da akwatinan dalibai da sauran Kayan dalibai wadda akayi kiyasin kudinsu yakai Naira Miliyan goma

Alhaji Mai Riga bai tsaya nan ba yace Gobarar Tashi takeyi a Jihar tamkar wutar yola a wurare daban daban wadda harzuwa lokacin da muke zantawa dashi yace Basu gama tantan ce Yawan hasarar dukiyar da aka samuba a fadin Jihar .

Sakataren Hukumar ta SEMA ya kara da cewar an sami Gobarar a kauyan larabar kuka dake karamar Hukumar kafin hausa da kuma wani kauye a karamar Hukumar Birniwa wadda yanzu haka ma aikatansa sunacan Suna tantance Yawan dukiyar data salwanta domin ganin gwamnati tabasu taimakon Gaggawa dazai ragewa wadanda abin yashafa Raɗaɗin.

Yakuma koka Akan karancin Kayan aiki da suka shafi Hukumar wadda ya hada da motocin daukar kaya da motar daukar marasa lafiya wato ambulance yace takai takawo idan za suje Rabon Kayan agajin Gaggawa dole sai sunyi Anfani daotocin haya kafin hakansu ya cimma ruwa wajan baiwa wadanda iftilai ya shafa agaji.

Saboda haka ya bukaci gwamnatin Jihar Jigawa ta samarwa Hukumar sema motocin daukar kaya kirar hilux tareda baiwa Hukumar motocin daukar marasa lafiya wato ambulance guda biyu domin bada agajin ceto ga wadanda iftilai ya rutsa dasu musamman a lokacin gobara .

Ya kuma bukaci gwamnan Jihar Alh Umar Namadi Dan modi yasa baki abasu motoci biyun da suke da bukata na ambulance dake ma aikatar lafiya a ajiye wadanda suke jibge wadanda aka sayesu lokacin cutar korona kuma ba ayin komai dasu ahain yanzu mai makon gwamnatin ta sake sayan wasu sabbi

Awaje daya kuma ya bukaci kungiyoyi Masu zaman kandi wato NGOs da sauran jama a Masu Hannu da shuni a Duk inda suke su shigo su agazawa Hukumar ta sema domin ganin aiyukan Hukumar yakai ga Nasara

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here